Domin daga gare ku ne aka baza Maganar Ubangiji, ba ma a ƙasar Makidoniya da ta Akaya kaɗai ba, har ma a ko'ina bangaskiyarku ga Allah ta shahara, har ma ya zamana, ba sai lalle mun faɗa ba.
Amma godiya ta tabbata ga Allah, shi da kullum yake yi mana jagaba mu ci nasara, albarkacin Almasihu, ta wurinmu kuma yake baza ƙanshin nan, na sanin Almasihu a ko'ina.