Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Korintiyawa 3:2 - Littafi Mai Tsarki

2 Ai, ku kanku ku ne wasiƙarmu ta yabo, wadda aka rubuta a zukatanku, domin kowa yă san ta, ya kuma karanta ta.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

2 Ai, ku kanku ku ne wasiƙarmu, wadda aka rubuta a zukatanku, domin kowa yă santa, yă kuma karanta ta.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Korintiyawa 3:2
9 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Domin daga gare ku ne aka baza Maganar Ubangiji, ba ma a ƙasar Makidoniya da ta Akaya kaɗai ba, har ma a ko'ina bangaskiyarku ga Allah ta shahara, har ma ya zamana, ba sai lalle mun faɗa ba.


Daidai ne kuwa a gare ni in riƙa tunaninku haka, ku duka, domin kuna a cikin zuciyata, domin dukanku abokan tarayya ne da ni da alherin Allah, ta wajen ɗaure ni da aka yi, da kuma ta yin kāriyar bishara da tabbatar da ita.


Da farko dai ina gode wa Allahna ta wurin Yesu Almasihu saboda ku duka, domin ana baza labarin bangaskiyarku a ko'ina a duniya.


Ni kam, zan kashe dukan abin hannuna da dukan zarafina da matuƙar farin ciki saboda ranku. In na ƙara ƙaunarku, ashe, sai a rage ƙaunata?


To, don me? Domin ba na ƙaunarku ne? Allah dai ya sani ina ƙaunarku.


Ba don in sa muku laifi na faɗi haka ba, don dā ma na gaya muku, abin ƙauna kuke a gare mu ƙwarai, ko a mace ko a raye, ba mu rabuwa.


Kamar gwanin magini, haka na sa harsashin gini, gwargwadon baiwar alherin da Allah ya yi mini, wani kuma yana ɗora gini a kai. Sai dai kowane mutum, yă lura da irin ginin da yake ɗorawa a kai.


Wato, har ila yau, yabon kanmu za mu fara yi kuma? Ko kuwa muna bukatar wasiƙun yabo ne zuwa gare ku, ko daga gare ku, kamar yadda waɗansu suke yi?


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ