Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Korintiyawa 3:10 - Littafi Mai Tsarki

10 Hakika a wannan hali, abin da dā take da ɗaukaka ya rasa ɗaukaka sam, saboda mafificiyar ɗaukakar da ta jice ta.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

10 Gama abin da dā take da ɗaukaka, ba ta da ɗaukaka a yanzu, in aka kwatantata da mafificiyar ɗaukaka ta yanzu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Korintiyawa 3:10
11 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Domin sa'ad da Allah Uba ya girmama shi, ya kuma ɗaukaka shi, sai murya ta zo masa daga mafificiyar ɗaukaka cewa, “Wannan shi ne Ɗana ƙaunataccena, wanda nake farin ciki da shi ƙwarai,”


Ba za a ƙara yin dare ba, ba za su bukaci hasken fitila, ko na rana ba, domin Ubangiji Allah zai haskaka su, za su kuma sha ni'imar Mulki har abada abadin.


da rana a tsaka a hanya, ya sarki, na ga wani haske ya bayyano daga sama, fiye da hasken rana, duk ya haskaka kewaye da ni da abokan tafiyata.


‘Wa ya ragu a cikinku da ya ga wannan Haikali da darajarsa ta dā? Ƙaƙa kuke ganinsa yanzu? A ganinku ba a bakin kome yake ba?


Wata zai duhunta, rana ba za ta ƙara haskakawa ba, domin Ubangiji Mai Runduna yake sarauta. Zai yi mulki a Urushalima a kan Dutsen Sihiyona, shugabannin jama'a za su dubi ɗaukakarsa.


Hasken wata ba haske ba ne a gare shi, Ko taurari ma ba su da tsarki a gabansa.


Gama idan hidimar da take jawo hukunci abar ɗaukakawa ce, to, lalle hidimar da take jawo samun adalcin Allah ta fi ta ɗaukaka nesa.


Domin in aba mai shuɗewa an bayyana ta da ɗaukaka, ashe, abin da yake dawwamamme, lalle ne ya kasance da ɗaukakar da ta fi haka nesa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ