8 Saboda haka, ina roƙonku ku tabbatar masa da ƙaunarku.
8 Saboda haka, ina roƙonku, ku sāke nuna masa ƙaunarku.
To, saboda haka, in hali ya yi, sai mu kyautata wa kowa, tun ba ma waɗanda suke jama'ar masu ba da gaskiya ba.
Ya ku 'yan'uwa, don 'yanci musamman aka kira ku, amma kada ku mai da 'yancin nan naku hujjar biye wa halin mutuntaka, sai dai ku bauta wa juna da ƙauna.
Gara dai ku yafe masa, ku kuma ƙarfafa masa zuciya, don kada gāyar baƙin ciki ya sha kansa.
Na rubuto muku wannan takanas, domin in jarraba ku, in ga ko kuna yin biyayya ta kowace hanya.