Ina tsoro kada watakila in na zo in same ku ba a yadda nake so ba, ku kuma ku gan ni ba a yadda kuke so ba, ko ma a tarar da jayayya, da kishi, da fushi, da sonkai, da yanke, da tsegunguma, da girmankai, da tashin hankali.
Ina rubuta wannan ne sa'ad da ba na tare da ku, domin sa'ad da na zo, kada ya zama mini tilas in yi muku tsanani a game da nuna ikon nan da Ubangiji ya ba ni saboda ingantawa, ba saboda rushewa ba.
Ku jarraba kanku ku gani, ko har yanzu kuna a raye da bangaskiya. Ku riƙa auna kanku. Ashe, ba ku tabbata Almasihu yana a cikinku ba? Sai ko in kun kasa ga gwajin!
Amma muna roƙon Allah kada ku yi wani mugun abu, ba don mu mu zama kamar mun ci gwajin kawai ba, sai dai domin ku yi abin da yake daidai, ko da yake za ku ga kamar mun kāsa.