13 Dukan tsarkaka suna gaishe ku.
Ina sa zuciya mu sadu ba da daɗewa ba, sa'an nan ma yi magana baka da baka.
'Ya'yan 'yar'uwarki zaɓaɓɓiya suna gaishe ki.
Ita da take a Babila, wadda ita ma zaɓaɓɓiya ce, ta aiko muku da gaisuwa. Haka kuma, ɗana, Markus.
Ku gai da dukan shugabanninku, da kuma dukan tsarkaka. Waɗanda suke daga ƙasar Italiya suna gaishe ku.
Ku gaggai da juna da tsattsarkar sumba. Dukan ikilisiyoyin Almasihu suna gaishe ku.
In kuwa 'yan'uwanku kaɗai kuke gayarwa, me kuka yi fiye da waɗansu? Ashe, ko al'ummai ma ba haka suke yi ba?