Almasihu, a lokacin zamansa a duniya, ya yi addu'o'i da roƙe-roƙe, tare da kuka mai tsanani, har da hawaye, ga wannan da yake da ikon cetonsa daga mutuwa, aka kuwa saurare shi saboda tsananin miƙa kansa.
Haka kuma Ruhu yake yi mana taimako a kan gajiyawarmu, domin ba mu ma san abin da ya kamata mu roƙa ba, amma Ruhu da kansa yana yi mana roƙo da nishe-nishen da ba su hurtuwa.
Amma da rigar, ko a tariyar zaren, ko a waɗarin, ko kowane abin da aka yi da fata, wanda cutar ta wanku daga shi sa'ad da aka wanke, sai a sāke wanke shi, ya kuwa zama tsarkakakke ke nan.