Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Korintiyawa 12:7 - Littafi Mai Tsarki

7 Don kada kaina yă kumbura kuma saboda mafifitan wahayan da aka yi mini, sai aka saka mini wata cuta, wadda ta zama mini ƙaya, jakadan Shaiɗan, don yă riƙa wahalshe ni, don kada kaina ya kumbura.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

7 Don kada in cika da girman kai saboda waɗannan mafifitan manyan wahayoyi, sai aka sa mini wata ƙaya a jikina wadda ta zama ɗan saƙon Shaiɗan, don ta wahalshe ni.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Korintiyawa 12:7
25 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Amma idan ba ku kori mazaunan ƙasar daga gabanku ba, to, waɗannan da kuka bari cikinta za su zama haki a idanunku, da ƙayayuwa a kwiyaɓunku. Za su yi ta wahalshe ku da yaƙi.


Don haka na ce, ‘Ba zan kore muku su ba, amma za su zamar muku ƙaya, gumakansu kuwa za su zamar muku tarko.’ ”


Kun dai sani a dalilin rashin lafiyata ne na yi muku bishara a zuwana na fari.


Amma sa'ad da ya kumbura, ya taurare ransa yana ta yin girmankai, sai aka kore shi daga gadon sarautarsa, aka raba shi kuma da darajarsa.


sai ku miƙa irin wannan mutum ga Shaiɗan, don yă hallaka jikinsa, ruhunsa kuma ya tsira a ranar Ubangiji Yesu.


Rana ta yi sama a sa'ad da Yakubu ya wuce Feniyel domin yana ɗingishi saboda kwatangwalonsa.


Sa'an nan Shaiɗan ya rabu da Ubangiji, ya je ya sa ƙuraje su fito ko'ina a jikin Ayuba.


Lalle ne kuma, kada yă zama sabon tuba, don kada yă daga kai yă burmu a cikin hukuncin da aka yi wa Iblis.


Amma sa'ad da ya yi ƙarfi, sai ya shiga girmankai, wanda ya zamar masa hallaka. Sai ya yi izgili a gaban Ubangiji Allahnsa, ya shiga Haikalin Ubangiji don ya ƙona turare a bisa bagaden ƙona turare.


to, sai ku lura, kada ku ɗaukaka kanku, har ku manta da Ubangiji Allahnku wanda ya fisshe ku daga ƙasar Masar, wato inda kuka yi bauta.


Sa'ad da mutumin ya ga bai rinjayi Yakubu ba sai ya taɓa kwarin kwatangwalonsa, sai gaɓar kwatangwalon Yakubu ta gulle a lokacin da yake kokawa da shi.


Don in wani ya sa ku bauta, kukan jure masa, ko ya yi muku ƙwace, ko ya more ku, ko ya nuna muka isa, ko kuwa ya mare ku.


Har a yanzu haka, yunwa muke ji, da ƙishirwa, muna huntanci, ana bugunmu, kuma yawo muke yi haka, ba mu da gida.


“ ‘A kan mutanen Isra'ila kuwa, al'ummai da suke kewaye da su, waɗanda suka raina su, ba za su ƙara zamar musu kamar sarƙaƙƙiya da ƙaya ba. Sa'an nan za su sani ni ne Ubangiji Allah.’


A kan 'yan saƙon sarakunan Babila kuwa, waɗanda aka aiko su don su bincika irin abin al'ajabi da ya faru a ƙasar, sai Allah ya ƙyale shi kurum don ya jarraba shi, ya san dukan abin da suke a zuciyarsa.


don kada zuciyarsa ta kumbura, har ya ga ya fi 'yan'uwansa, don kuma kada ya karkace daga bin umarni zuwa dama ko hagu, don shi da 'ya'yansa su daɗe, suna mulki a Isra'ila.”


Muna ka da masu hujjoji a cikin zace-zacensu, muna rushe kowace ganuwar alfarma mai tare sanin Allah, muna kuma jan hankalin kowa ga bautar Almasihu.


Ashe, bai kamata matar nan 'yar zuriyar Ibrahim, wadda Shaiɗan ya ɗaure, yau shekara goma sha takwas, a kwance ta daga wannan ƙuƙumi a ran Asabar ba?”


Sai suka tattofa masa yau a fuska, suka bubbuge shi, waɗansu kuma suka mammare shi,


Ubangiji ya ce wa Shaiɗan, “Shi ke nan, yana cikin ikonka, amma fa, kada ka kashe shi.”


“Don haka zan shinge hanyarta da ƙaya, Zan gina mata garu don kada ta sami hanyar fita.


Sai Yesu ya ce masa, “Tafi daga nan, kai Shaiɗan! domin a rubuce yake cewa, ‘Kă yi wa Ubangiji Allahnka sujada, Shi kaɗai za ka bauta wa.’ ”


Don waɗansu suna cewa, “Wasiƙunsa masu ratsa jiki ne, masu ƙarfi, amma kuwa in ka gan shi ba shi da kwarjini, maganarsa kuma ba wata magana ba ce.”


An tilasta mini ne in yi gadara, ko da yake ba ta amfane ni da kome ba. Amma zan ci gaba da zancen ruya da wahayi da Ubangiji ya yi mini.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ