Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Korintiyawa 12:6 - Littafi Mai Tsarki

6 Ko da zan so yin gadara ma, ba zan zama wawa ba, gama gaskiya zan faɗa. Amma na bar zancen haka, don kada wani ya ɗauke ni fiye da yadda yake ganina, ko yadda yake jin maganata.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

6 Ko da zan so yin gadara ma, ba zan zama wawa ba, gama gaskiya zan faɗa. Amma na bar zancen haka, don kada wani ya ɗauke ni fiye da yadda yake ganina, ko yadda yake jin maganata.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Korintiyawa 12:6
12 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ina sāke faɗa, kada wani ya zaci ni wawa ne. In kuwa kun zaci haka nake, to, ku ji ni wawa ne, don ni ma in samu in taɓa 'yar taƙama kaɗan.


Na yi wauta kam, amma ku ne kuke tilasta mini, ku ne kuwa ya kamata ku yaba mini, domin ba inda na kasa waɗannan mafifitan manzanni, ko da yake ni ba kome ba ne.


Allahn Ubangiji Yesu, wato Ubansa, wanda ya yabo ya tabbata a gare shi har abada, ya sani ba ƙarya nake yi ba.


Don kada kaina yă kumbura kuma saboda mafifitan wahayan da aka yi mini, sai aka saka mini wata cuta, wadda ta zama mini ƙaya, jakadan Shaiɗan, don yă riƙa wahalshe ni, don kada kaina ya kumbura.


In hankalinmu ya fita, ai, saboda Allah ne, in kuwa a cikin hankalinmu muke, ai, ribarku ce.


Yadda ba shakka Allah yake mai alkawari, haka ma maganar da muka yi muku, ba shiririta a ciki.


To, wane ne Afolos? wane ne Bulus kuma? Ashe, ba bayi ne kawai ba, waɗanda kuka ba da gaskiya ta wurinsu, ko wannensu kuwa gwargwadon abin da Ubangiji ya ba shi?


Gaskiya nake faɗa, ni na Almasihu ne, ba ƙarya nake yi ba. Lamirina, ta wurin Ruhu Mai Tsarki, yana ba da shaida,


Akwai wanda zai iya cewa, ba haka ba ne? Akwai wanda zai tabbatar da cewa kalmomina ba gaskiya ba ne?”


Don ko da na gaya masa cewa, ina 'yar taƙama da ku, ban kunyata ba. Kamar yadda duk abin da muka gaya muku gaskiya ne, haka kuma taƙamarmu da ku a idon Titus ma ta zama gaskiya.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ