Na roƙi Titus ya je, na kuma aiko ɗan'uwan nan tare da shi. To, Titus ya cuce ku ne? Ashe, ba Ruhu ɗaya yake bi da mu ba, ni da shi? Ba kuma hanya ɗaya muke bi ba?
Saboda haka, na dai ga lalle ne in roƙi 'yan'uwan nan su riga ni zuwa a gare ku, su tanada baiwar nan da kuka yi alkawari kafin in zo, domin a same ta a shirye, ba tare da matsawa ba, sai dai kyautar sa kai.
Saboda haka, na aika muku da Timoti, wanda yake shi ne ɗana ƙaunatacce, amintacce kuma a cikin Ubangiji, zai kuwa tuna muku da ka'idodina na bin Almasihu, kamar yadda nake koyarwa a ko'ina, a kowace ikkilisiya.