Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Korintiyawa 11:7 - Littafi Mai Tsarki

7 Ashe, laifi na yi da na ƙasƙantar da kaina, don a ɗaukaka ku, wato, saboda na yi muku bisharar Allah a kyauta?

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

7 Laifi ke nan ne na yi da na ƙasƙantar da kaina, don a ɗaga ku zuwa babban matsayi ta wurin yin muku wa’azin bisharar Allah kyauta?

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Korintiyawa 11:7
14 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ta wace hanya ce kuka kasa sauran ikkilisiyoyi? Ko kuwa domin dai ni ban nauyaya muku ba? To, ku yafe mini wannan laifi!


Ya ku 'yan'uwa, kuna iya tunawa da wahala da famar da muka sha, har muna aiki dare da rana, don kada mu nauyaya wa kowane ɗayanku, duk sa'ad da muke yi muku bisharar Allah.


Ni Bulus da kaina, ina roƙonku albarkacin tawali'u da sanyin hali na Almasihu, ni da ake yi wa kirari “marar tsanani” ne a cikinku, amma “mai matsawa” ne sa'ad da nake rabe da ku,


Ko kuwa dai ni da Barnaba ne kawai, ba mu da iko a ɗauke mana aikin ci da kai?


ba mu kuwa ci abincin kowa a banza ba, sai dai mun sha wahala da fama, muna aiki dare da rana, don kada mu nawaita wa kowane ɗayanku.


Ku da kanku kun sani hannuwan nan nawa su suka biya mini bukace-bukacena, da na waɗanda suke tare da ni.


Da yake waɗansu sun mori halaliyarsu a game da ku, ashe ba mu muka fi cancanta ba? Duk da haka ba mu mori wannan halaliya ba, sai dai muna jure wa kome, don ta koƙaƙa kada mu hana bisharar Almasihu yaɗuwa.


Ban yi ƙyashin kuɗin kowa ba, ko kuwa tufafin wani.


Daga Bulus, bawan Yesu Almasihu, manzo kirayayye, keɓaɓɓe domin yin bisharar Allah,


To, sa'ad da na zo Taruwasa in yi bisharar Almasihu, ko da yake an buɗe mini hanya a cikin Ubangiji,


har ma mu samu mu yi bishara a ƙasashen da suke a gaba da ku, ba tare da wata fahariya da aikin da wani ya riga ya yi a fagensa ba.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ