Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Korintiyawa 11:26 - Littafi Mai Tsarki

26 Na yi tafifiya da yawa, na sha hatsari a koguna, na sha hatsarin 'yan fashi, na sha hatsari a hannun kabilarmu, na sha hatsari a hannun al'ummai, na sha hatsari a birane, na sha hatsari a jeji, na sha hatsari a bahar, na kuma sha hatsarin 'yan'uwa na ƙarya.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

26 Na yi tafiye-tafiye da yawa, na sha hatsari a koguna, na sha hatsarin ’yan fashi, na sha hatsari a hannun kabilarmu, na sha hatsari a hannun al’ummai, na sha hatsari a birane, na sha hatsari a jeji, na sha hatsari a teku, na kuma sha hatsarin ’yan’uwa na ƙarya.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Korintiyawa 11:26
35 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sa'ad da al'ummai da Yahudawa tare da shugabanninsu suka tasar wa manzannin, su wulakanta su, su jejjefe su da duwatsu,


ya kyauta musu, ya aika a zo da shi Urushalima, alhali kuwa sun shirya 'yan kwanto su kashe shi a hanya.


ina bauta wa Ubangiji da matuƙar tawali'u, har da hawaye, da gwaggwarmaya iri iri da na sha game da makircin Yahudawa.


Amma Yahudawa, saboda kishi, suka ɗibi waɗansu ashararai, 'yan iska, suka tara jama'a suka hargitsa garin kaf, suka fāɗa wa gidan Yason, suna nemansu don su fito da su gaban taron jama'a.


Amma Yahudawa suka zuga waɗansu mata masu ibada, masu daraja, da kuma waɗansu manyan gari, suka haddasa tsanani ga Bulus da Barnaba, suka kore su daga ƙasarsu.


Maganar nan ta tashi saboda 'yan'uwan ƙaryar nan ne, da aka shigo da su a asirce, waɗanda suka saɗaɗo su yi ganganen 'yancinmu da muke da shi ta wurin Almasihu Yesu, don dai su sa mu bauta.


A Dimashƙu gwamnan da yake ƙarƙashin sarki Aretis ya tsare ƙofofin birnin Dimashƙu don ya kama ni,


Idan bisa ga ra'ayin mutum ne, na yi kokawa da namomin jeji a Afisa, mece ce ribata in dai har ba a ta da matattu? “Ba sai mu yi ta ci da sha ba, da yake gobe za mu mutu?”


ta wurin ikon mu'ujizai, da abubuwan al'ajabai, da kuma ta wurin ikon Ruhun, har dai daga Urushalima da kewayenta, har zuwa Ilirikun, na yi bisharar Almasihu a ko'ina.


Da gardamar ta yi tsanani, don gudun kada su yi kaca-kaca da Bulus, shugaban ya umarci sojan su sauka su ƙwato shi daga wurinsu ƙarfi da yaji, su kawo shi a kagarar soja.


A lokacin nan kuwa ba ƙaramin hargitsi aka yi game da wannan hanya ba.


To, lokacin da Afolos yake Koranti, Bulus ya zazzaga ƙasar ta kan tudu, ya gangara zuwa Afisa. A can ya tarar da waɗansu masu bi,


Amma sa'ad da Galiyo yake muƙaddashin ƙasar Akaya, Yahudawa suka tasar wa Bulus da nufi ɗaya suka kawo shi a gaban shari'a,


amma Bulus ya zaɓi Sila, bayan 'yan'uwa sun yi masa addu'a alherin Allah ya kiyaye shi, ya tafi.


Amma waɗansu Yahudawa suka zo daga Antakiya da Ikoniya, da suka rarrashi taron, suka jejjefe Bulus suka ja shi bayan gari, suna zato ya mutu.


Amma da Yahudawa suka ga taro masu yawa, suka yi kishi gaya, suka yi ta musun abubuwan da Bulus ya faɗa, suna zaginsa.


Amma da Yahudawan Tasalonika suka ji labari Bulus yana sanar da Maganar Allah a Biriya ma, suka je suka zuga taro masu yawa a can ma, suna ta da hankalinsu.


ya yi wata uku a nan. Da Yahudawa suka ƙulla masa makirci, a sa'ad da zai tashi a jirgin ruwa zuwa ƙasar Suriya, ya yi niyyar komawa ta ƙasar Makidoniya.


Sai sojan suka yi niyya su kashe 'yan sarka, don kada wani ya yi ninƙaya ya tsira.


Wa zai iya raba mu da ƙaunar da Almasihu yake yi mana? Ƙunci ne? ko masifa? ko tsanani? ko yunwa? ko huntanci? ko hatsari? ko takobi?


Don me kuma nake a cikin hatsari a kowane lokaci?


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ