Yesu ya faɗa masa, faɗa ta uku, “Bitrus ɗan Yahaya, kana sona?” Sai Bitrus ya yi baƙin ciki don a faɗar nan ta uku ya ce masa, “Kana sona?” Shi kuwa ya ce masa, “Ya Ubangiji, ai, ka san kome duka, ka kuwa sani ina sonka.” Yesu ya ce masa, “Ka yi kiwon tumakina.
“Allah Maɗaukaki, Allah Ubangiji ya sani, bari Isra'ilawa kuma da kansu su sani. Idan tayarwa ce, ko kuwa mun yi wa Ubangiji rashin aminci ne, to, kada ku bar mu da rai yau.
Domin mu ba kamar mutane da yawa muke ba, masu yi wa Maganar Allah algus, mu kaifi ɗaya ne, kamar yadda Allah ya umarce mu, haka muke magana a gaban Allah, muna na Almasihu.