Don in wani ya zo yana wa'azin wani Yesu dabam da wanda muka yi wa'azi, ko kuma in kun sami wani ruhu dabam da Ruhun da kuka samu, ko wata bishara dabam da wadda kuka yi na'am da ita, ashe, har kuna saurin yin na'am da irinsu ke nan!
Da yake bisa ga hikimar Allah, duniya ba ta san Allah ta wurin hikimarta ba, sai Allah ya ji daɗin ceton masu ba da gaskiya, ta wurin wautar shelar bishara.
Na yi wauta kam, amma ku ne kuke tilasta mini, ku ne kuwa ya kamata ku yaba mini, domin ba inda na kasa waɗannan mafifitan manzanni, ko da yake ni ba kome ba ne.
An ɗauke mu marasa azanci saboda Almasihu, wato, ku kuwa masu azanci cikin Almasihu! Wato, mu raunana ne, ku kuwa ƙarfafa! Ku kam, ana ganinku da martaba, mu kuwa a wulakance!
Mhm, wato, har kun riga kun yi hamdala! Har kun wadata! Har ma kun yi sarauta ba tare da mu ba ma! Da ma a ce kun yi mulki mana, har mu ma mu yi tare da ku!
Kada kowa yă ruɗi kansa. In waninku ya zaci shi mai hikima ne, yadda duniya ta ɗauki hikima, sai yă mai da kansa marar hikima, domin ya sami zama mai hikima.
Bulus kuwa ya ce, “Ko a ɗan wannan, ko a mai yawa, ina fata ga Allah, ba kai kaɗai ba, har ma duk waɗanda suke saurarona a yau, su zama kamar yadda nake, sai dai banda sarƙar nan.”
Sai Yesu ya amsa ya ce, “Ya ku marasa bangaskiya, kangararru na wannan zamani! Har yaushe zan zama da ku? Har yaushe kuma zan jure muku? Ku kawo mini shi nan.”
Joshuwa ya ce, “Kaitonmu, ya Ubangiji Allah, me ya sa ka haye da jama'an nan zuwa wannan hayin Urdun, don ka bashe mu a hannun Amoriyawa, su hallakar da mu? Da ma mun haƙura, mun yi zamanmu a wancan hayin Urdun.