Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Korintiyawa 10:4 - Littafi Mai Tsarki

4 Don kuwa makamanmu na fama ba na mutuntaka ba ne, na ikon Allah ne, masu rushe maƙamai masu ƙarfi.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

4 Makaman da muke yaƙi da su, ba makamai na duniya ba ne. Sai dai na ikon Allah ne, masu rushe wuraren mafaka masu ƙarfi.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Korintiyawa 10:4
28 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

da maganar gaskiya, da kuma ikon Allah. Muna riƙe da makaman adalci dama da hagu.


Ga shi, a wannan rana na ba ka iko a kan al'ummai da mulkoki, Don ka tumɓuke, ka rusar, Ka hallakar, ka kaɓantar, Ka gina, ka dasa.”


kada bangaskiyarku ta dogara ga hikimar mutane, sai ga ƙarfin Allah.


Na danƙa maka wannan umarni, ya ɗana Timoti, bisa ga annabce-annabcen da dā aka faɗa a kanka, domin ka ƙarfafu ta wurinsu, ka yi yaƙi mai kyau,


Dare fa ya ƙure, gari ya kusa wayewa. Sai mu watsar da ayyukan duhu, mu yi ɗamara da kayan ɗamara na haske.


Amma da yake mu na rana ne, sai mu natsu, muna saye da sulken bangaskiya da ƙauna, muna begen samun ceto, shi ne kuma kwalkwakinmu.


Wannan wadata da muke da ita kuwa, a cikin kasake take, wato, jikunanmu, don a nuna mafificin ikon nan na Allah ne, ba namu ba.


Kada kuma ku miƙa gaɓoɓinku su zama kayan aikin mugunta, don yin zunubi. Amma ku miƙa kanku ga Allah, kamar waɗanda aka raya bayan mutuwa, kuna miƙa gaɓoɓinku ga Allah kayan aikin adalci.


Ba domin mun isar wa kanmu ba ne, har da za mu ce mu ne muke gudanar da wani abu, a'a, iyawarmu daga Allah take,


Tun daga Sihiyona Ubangiji zai faɗaɗa sarautarka, ya ce, “Ka yi mulki bisa maƙiyanka.”


Ta wurin bangaskiya garun Yariko ya rushe, bayan an yi ta kewaya shi har kwana bakwai.


Kai kuma ka jure wa shan wuya, kana amintaccen sojan Almasihu Yesu.


Sai aka karantar da Musa dukan ilimin Masarawa, shi kuwa mutum mai iko ne a cikin magana da ayyukansa.


A wannan rana sa'ad da aka kame kagaran abokan gābanku, aka kashe jama'arsu, rafuffukan ruwa za su malalo daga kowane tsauni da kowane tudu.


Jama'a suka yi ihu, aka busa ƙahoni. Nan da nan da jama'ar suka ji muryar ƙaho, suka yi ihu da babbar murya, sai garun ya rushe tun daga tushenta. Jama'a kuwa suka shiga birnin, kowanne ya nufi inda ya fuskanta sosai, suka ci birnin.


Ina rubuta wannan ne sa'ad da ba na tare da ku, domin sa'ad da na zo, kada ya zama mini tilas in yi muku tsanani a game da nuna ikon nan da Ubangiji ya ba ni saboda ingantawa, ba saboda rushewa ba.


Wa yake yin aikin soja, sa'an nan yă ci da kansa? Wa zai shuka garkar inabi, yă kasa cin 'ya'yan? Wa zai yi kiwon garke, yă kasa shan nonon?


Maganata kamar wuta ce, kamar guduma mai farfashe dutse. Ni Ubangiji na faɗa.


Ko da zan yi gadara fiye da kima a game da izinin nan namu, wanda Ubangiji ya bayar saboda inganta ku, ba don rushe ku ba, ba zan kunyata ba.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ