An gicciye ni tare da Almasihu. Yanzu ba ni ne kuma nake a raye ba, Almasihu ne yake a raye a cikina. Rayuwar nan kuma da nake yi ta jiki, rayuwa ce ta wurin bangaskiya ga Ɗan Allah, wanda ya ƙaunace ni, har ya ba da kansa domina.
Saboda haka, tun da taron shaidu masu ɗumbun yawa suka kewaye mu haka, sai mu ma mu yar da dukkan abin da ya nauyaya mana, da kuma zunubin da ya ɗafe mana, mu kuma yi tseren nan da yake gabanmu tare da jimiri,
Ashe, a lokacin da na yi niyyar yin haka, wato na nuna rashin tsai da zuciya ke nan? Ko kuwa shiririta nake yi kawai irin ta halin mutuntaka, in ce, “I” in koma in ce, “A'a”?