Dukan wanda yake so ya roƙi albarka, sai ya roƙi Allah ya sa masa albarka, Allah da yake mai aminci ne. Dukan wanda zai sha rantsuwa, sai ya rantse da sunan Allah, Allah da yake mai aminci ne. Wahalan dā za su ƙare, za a kuwa manta da su.”
Idan kun yi rantsuwa kuka ce, ‘Har da ran Ubangiji kuwa,’ Da gaskiya, da aminci, da adalci, Sa'an nan sauran al'umma za su so in sa musu albarka, Za su kuma yabe ni.”
Za ku watsa su sama cikin iska, Iska za ta hure su, ta tafi da su, Hadiri kuma zai warwatsar da su. Amma za ku yi murna, gama ni ne Allahnku, Za ku yabe ni, Allah Mai Tsarki na Isra'ila.
Ka yardar mini in ga wadatar jama'arka, In yi tarayya da jama'arka da farin cikinsu, In yi farin ciki tare da waɗanda suke murna ta fāriya domin su naka ne.