Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Korintiyawa 10:10 - Littafi Mai Tsarki

10 Don waɗansu suna cewa, “Wasiƙunsa masu ratsa jiki ne, masu ƙarfi, amma kuwa in ka gan shi ba shi da kwarjini, maganarsa kuma ba wata magana ba ce.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

10 Gama waɗansu suna cewa, “Wasiƙunsa suna da nauyi da kuma ƙarfi, amma kuwa in ka gan shi, ba shi da wani kwarjini, maganarsa kuma ba kome ba ce.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Korintiyawa 10:10
13 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ai, ba don in yi baftisma Almasihu ya aiko ni ba, sai dai in sanar da bishara, ba kuwa da gwanintar iya magana ba, domin kada a wofinta ƙarfin gicciyen Almasihu.


Ko da yake ni bāmi ne a wajen yin magana, a wajen sani kam, ba haka ba ne, mun kuwa bayyana wannan sarai ta kowace hanya a cikin dukan sha'aninmu da ku.


Amma Musa ya ce wa Ubangiji, “Ya Ubangijina, ni ba mai lafazi ba ne, ban taɓa zama ba, ko a yanzu ma, bayan da ka yi magana da bawanka, gama ni mai nauyin baki ne, mai nauyin harshe kuma.”


Ni Bulus da kaina, ina roƙonku albarkacin tawali'u da sanyin hali na Almasihu, ni da ake yi wa kirari “marar tsanani” ne a cikinku, amma “mai matsawa” ne sa'ad da nake rabe da ku,


Da yake bisa ga hikimar Allah, duniya ba ta san Allah ta wurin hikimarta ba, sai Allah ya ji daɗin ceton masu ba da gaskiya, ta wurin wautar shelar bishara.


Sai na ce, “Ya Ubangiji Allah! Ban san abin da zan faɗa ba, Gama ni yaro ne.”


Kada fa a ga kamar ina tsorata ku da wasiƙu ne.


Irin mutanen nan dai su fahimci yadda abin da muke faɗa a cikin wasiƙa sa'ad da ba ma nan, shi muke aikatawa sa'ad da muke nan.


Mu kam, saboda rauninmu, wane mu da yin haka! Amma ta ko yaya wani yake ƙarfin halin yin fariya, ina magana a kan ni wawa ne fa! to, ni ma sai in yi.


In dai nema kuke yi ku tabbata, cewa da izinin Almasihu nake magana, to, ai, shi ba rarrauna ba ne a gare ku, amma ƙaƙƙarfa ne a cikinku.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ