Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Korintiyawa 1:8 - Littafi Mai Tsarki

8 'Yan'uwa, ba ma so ku jahilta da wahalar da muka sha a ƙasar Asiya, domin kuwa mun ji jiki ƙwarai da gaske, har abin ya fi ƙarfinmu, har ma muka fid da tsammanin rayuwa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

8 ’Yan’uwa, ba ma so ku zama da rashin sani, a kan wahalolin da muka sha a lardin Asiya. Mun sha wahaloli sosai, har abin ya fi ƙarfinmu, ya sa muka fid da tsammanin rayuwa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Korintiyawa 1:8
13 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Idan bisa ga ra'ayin mutum ne, na yi kokawa da namomin jeji a Afisa, mece ce ribata in dai har ba a ta da matattu? “Ba sai mu yi ta ci da sha ba, da yake gobe za mu mutu?”


Mhm, wato, har kun riga kun yi hamdala! Har kun wadata! Har ma kun yi sarauta ba tare da mu ba ma! Da ma a ce kun yi mulki mana, har mu ma mu yi tare da ku!


Don kuwa, an buɗe mini wata hanya mai fāɗi ta yin aiki mai amfani, akwai kuma magabta da yawa.


Dawuda ya yi tunani a ransa, ya ce, “Wata rana Saul zai kashi ni, don haka ba abin da ya fi mini, sai in tsere zuwa ƙasar Filistiyawa. Sa'an nan Saul zai fid da zuciya ga nemana a ƙasar Isra'ila. Zan kuwa tsira daga hannunsa.”


Amma Dawuda ya rantse masa, ya ce, “Mahaifinka ya hakikance na sami tagomashi a wurinka, domin haka ba zai sanar maka da wannan ba, don kada ya baƙanta maka rai. Na rantse da Ubangiji da kai kuma, mataki ɗaya yake tsakanina da mutuwa!”


Ga mu kuwa, Fartiyawa, da Madayanawa, da Elamawa, da mutanen ƙasar Bagadaza, da na Yahudiya, da na Kafadokiya, da na Fantas, da na Asiya,


Sai suka zazzaga ƙasar Firijiya da ta Galatiya, saboda Ruhu Mai Tsarki ya hana su yin Maganar Ubangiji a ƙasar Asiya.


Ina so ku sani 'yan'uwa, na sha ɗaura niyyar zuwa wurinku, ko da yake har yanzu ba a yardar mini ba, domin ku ma in sami amfani a gare ku, kamar yadda na samu a cikin al'ummai.


Har ma muka ji kamar hukuncin kisa aka yi mana, wannan kuwa don kada mu dogara ga kanmu ne, sai dai ga Allah, mai ta da matattu.


Kamar ma ba a san mu ba, an kuwa san mu sarai, kamar a bakin mutuwa muke, ga shi kuwa, muna a raye, ana ta horonmu, duk da haka ba a kashe mu ba,


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ