Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Bitrus 3:4 - Littafi Mai Tsarki

4 suna cewa, “To, ina alkawarin dawowarsa? Ai, tun a lokacin da kakannin kakanninmu suka ƙaura, dukan abubuwa suna tafe ne kamar dā, tun farkon halitta.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

4 Za su ce, “Ina wannan ‘dawowar’ da ya yi alkawari ne? Tun mutuwar kakanninmu, kome yana tafiya kamar yadda yake tun farkon halitta.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Bitrus 3:4
20 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ga shi, suna ce mini, “Ina maganar Ubangiji take? Ta zo mana!”


Kun gajiyar da Ubangiji Mai Runduna da maganganunku, amma kun ce, “Ƙaƙa muka gajiyar da shi?” Kuna cewa, “Ubangiji yana ganinsu, dukan masu aikata mugunta mutanen kirki ne, yana kuwa ƙaunarsu.” Kuna kuma cewa, “Ina Allah yake wanda yake shi adali ne?”


In kuwa bawan nan ya ce a ransa, ‘Ubangijina ya jinkirta zuwansa,’ sa'an nan ya soma dūkan barori, maza da mata, ya shiga ci da sha har yana buguwa,


Don me mutane suke aikata laifofi a natse? Domin ba a hukunta laifofi nan da nan.


Amma in bawan nan mugu ne, ya kuma ce a ransa, ‘Ubangidana ya jinkirta zuwansa,’


Su wane ne abin sa zuciyarmu, da abin farin cikinmu, da kuma abin taƙamarmu a gaban Ubangiji Yesu a ranar komowarsa, in ba ku ba?


Sai Lutu ya fita ya faɗa wa surukansa waɗanda za su auri 'ya'yansa mata, “Tashi, ku fita daga wannan wuri, gama Ubangiji yana gab da hallaka birnin.” Amma sai surukansa suka aza wasa yake yi.


A lokacin nan za a yi wata matsananciyar wahala, irin wadda ba a taɓa yi ba tun farkon halittar da Allah ya yi, har ya zuwa yanzu, ba kuwa za a ƙara yi ba har abada.


Abin da ya faru a dā, shi zai sāke faruwa, Abin da aka yi a dā, shi za a sāke yi. A duniya duka ba wani abu da yake sabo.


“Ka kuma rubuta wa mala'ikan ikkilisiyar da take a Lawudikiya haka, ‘Ga maganar tabbataccen nan, Amintaccen Mashaidi mai gaskiya, wanda ta wurinsa dukkan halittar Allah ta kasance.


Waɗanda suke cewa, ‘Lokacin gina gidaje bai yi kusa ba. Wannan birni tukunya ce mai ɓararraka, mu ne kuwa naman.’


Amma tun farkon halitta ‘Allah ya halicce su, namiji da tamata.’


Inda mushe yake, ai, a nan ungulai sukan taru.


Domin Ɗan Mutum zai zo da ɗaukakar Ubansa tare da mala'ikunsa. A sa'an nan ne zai sāka wa kowane mutum gwargwadon aikinsa.


Hakika, ina gaya muku, akwai waɗansu tsaitsaye a nan da ba za su mutu ba, sai sun ga Ɗan Mutum yana zuwa cikin Mulkinsa.”


Sa'an nan ya durƙusa, ya ɗaga murya da ƙarfi, ya ce, “Ya Ubangiji, kada ka ɗora musu wannan zunubi.” Da faɗar haka sai ya yi barci.


kuna sauraron ranar Allah, kuna gaggauta zuwanta! Da zuwanta kuwa za a kunna wa sammai wuta, su hallaka, dukkan abubuwa kuma da suke a cikinsu, wuta za ta narkar da su.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ