Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Bitrus 3:18 - Littafi Mai Tsarki

18 Amma ku ƙaru da alherin Ubangijinmu, Mai Cetonmu Yesu Almasihu da kuma saninsa. Ɗaukaka tă tabbata a gare shi a yanzu, da kuma har abada. Amin! Amin!

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

18 Sai dai ku yi girma cikin alheri da sanin Ubangijinmu da Mai Cetonmu Yesu Kiristi. A gare shi ɗaukaka ta tabbata yanzu da har abada! Amin.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Bitrus 3:18
26 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

domin ku yi zaman da ya cancanci bautar Ubangiji, kuna faranta masa ta kowane fanni, kuna ba da amfani a kowane aiki nagari, kuna ƙaruwa da sanin Allah.


A maimakon haka, sai mu faɗi gaskiya game da ƙauna, muna girma a cikinsa ta kowace hanya, wato Almasihu, shi da yake shugabanmu.


Kamar jariri sabon haihuwa, ku yi marmarin shan madara marar gami mai ruhu, domin ku girma da shi, har ya kai ku ga samun ceto,


Dahir na ɗauki dukkan abubuwa hasara ne, a kan mafificiyar darajar sanin da nake yi na Almasihu Yesu Ubangijina. Saboda shi ne na zaɓi yin hasarar dukkan abubuwa, har ma na mai da su tozari domin Almasihu yă zama nawa,


da nufin cewa Allah na Ubangijinmu Yesu Almasihu, Uba Maɗaukaki, yă ba ku Ruhu mai ba da hikima da bayani ga sanin Allah,


kun ɗauki sabon halin nan da ake sabuntawa ga sani, bisa ga kamannin Mahaliccinsa.


Allah da ikonsa yā yi mana baiwa da dukan abubuwan da suka wajaba ga rayuwa da kuma binsa, ta sanin wanda ya kira mu ga samun ɗaukakarsa da fifikonsa,


Domin shi Allah wanda ya ce, “Haske yă ɓullo daga duhu ya haskaka,” shi ne ya haskaka zukatanmu domin a haskaka mutane su san ɗaukakarsa a fuskar Yesu Almasihu.


Ubangiji zai cece ni daga kowane mugun abu, ya kuma kiyaye ni, ya kai ni ga Mulkinsa na Sama. Ɗaukaka tă tabbata a gare shi har abada abadin. Amin! Amin!


Rai madawwami kuwa, shi ne su san ka, Allah Makaɗaici na gaskiya, da kuma Yesu Almasihu da ka aiko.


Adalai za su yi yabanya Kamar itatuwan giginya, Za su yi girma kamar itatuwan al'ul na Lebanon.


Lalle ne a kullum mu gode wa Allah saboda ku, 'yan'uwa, haka kuwa ya kyautu, da yake bangaskiyarku haɓaka take yi ƙwarai da gaske, har ma ƙaunar kowane ɗayanku ga juna ƙaruwa take yi.


Ai, daga gare shi ne, ta wurinsa kuma, dukkan abubuwa suke, shi ne kuma makomarsu. Ɗaukaka tă tabbata a gare shi har abada. Amin.


ya mai da mu firistoci, mallakar Allah Ubansa. Amin.


ga Allah makaɗaici Mai Cetonmu ta wurin Yesu Almasihu Ubangijinmu, ɗaukaka, da fifiko, da mulki, da iko su tabbata gare shi, tun fil'azal, da yanzu, da kuma har abada abadin. Amin, amin.


Ta haka kuma, za a ba ku cikakken 'yancin shiga madawwamin mulki na Ubangijinmu Mai Cetonmu Yesu Almasihu.


In kuwa bayan da suka tsere wa ƙazantar duniyar albarkacin sanin Ubangijinmu, Mai Cetonmu Yesu Almasihu, suka kuma sāke sarƙafewa a ciki, har aka rinjaye su, ƙarshen zamansu ya fi na fari lalacewa ke nan.


In kuwa halayen nan sun zama naku ne, har suna yalwata, za su sa ku kada ku yi zaman banza, ko marasa amfani a wajen sanin Ubangijinmu Yesu Almasihu.


kuna koya musu su kiyaye duk iyakar abin da na umarce ku. Ga shi, ni kuma kullum ina tare da ku har zuwa matuƙar zamani.”


Kada ka kai mu wurin jaraba, Amma ka cece mu daga Mugun.’


Amma ku da kuke yi mini biyayya, ikon cetona zai fito muku kamar rana. Zai kawo warkarwa kamar hasken rana. Za ku fita kuna tsalle kamar 'yan maruƙan da aka fisshe su daga garke.


Zan zama kamar raɓa ga Isra'ila, Isra'ila za ta yi fure kamar lili, Saiwarta za ta shiga kamar itacen al'ul.


domin kowa yă girmama Ɗan, kamar yadda ake girmama Uban. Wanda ba ya girmama Ɗan, ba ya girmama Uban da ya aiko shi ke nan.


Alheri da salama su yawaita a gare ku, a wajen sanin Allah da Yesu Ubangijinmu


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ