Amma mutanen nan sukan kushe duk abin da ba su fahinta ba, saboda abubuwan da suka sani bisa ga jiki suna kamar dabbobi marasa hankali, su ne kuwa sanadin halakarsu.
Tana kuma yaudarar mazaunan duniya, da abubuwan al'ajabin nan da aka yardar mata ta yi a gaban dabbar nan, tana umartarsu, su yi wata siffa saboda dabbar nan wadda aka yi wa rauni da takobi, ta kuwa rayu.
don ya zartar da hukunci kan kowa, yă kuma tabbatar wa marasa bin Allah dukan aikinsu na rashin bin Allah, da suka aikata ta hanyar rashin bin Allah, da kuma baƙaƙen maganganu da masu zunubi marasa bin Allah suka yi game da shi.”
Ku yi halin yabo a cikin al'ummai, don duk sa'ad da suke kushenku, cewa ku mugaye ne, sai su ga kyawawan ayyukanku, har su ɗaukaka Allah a ran da alheri ya sauko musu.
Amma na yarda cewa, bisa ga hanyar nan da suke kira ‘Ɗariƙa’ nake bauta wa Allahn kakanninmu, nake kuma gaskata duk abin da yake a rubuce a cikin Attaura da kuma littattafan annabawa.
Sai aka jefa ƙaton macijin nan a ƙasa, wato macijin nan na tun dā dā, wanda ake kira Ibilis da Shaiɗan, mayaudarin dukkan duniya, aka jefa shi a duniya, mala'ikunsa ma aka jefa su tare da shi.
Saboda haka, ina so gwauraye masu ƙuruciya waɗanda mazansu suka mutu su yi aure, su haifu, su tafiyar da al'amuran gida, kada su ba magabci hanyar zarginmu.
Amma da waɗansu suka taurare, suka ƙi ba da gaskiya, suna kushen wannan hanya gaban jama'a, sai ya rabu da su, ya keɓe masu bi, yana ta muhawwara da su a kowace rana makarantar Tiranas.
Sai ya fara wa'azi gabagaɗi a majami'a, amma da Bilkisu da Akila suka ji maganarsa, suka ja shi a jika, suka ƙara bayyana masa tafarkin Allah sosai da sosai.
Da suka zo, suka ce masa, “Malam, ai, mun sani kai mai gaskiya ne, ba ka kuma zaɓen kowa, domin ka ɗauki kowa da kowa daidai, sai koyar da tafarkin Allah sosai kake yi. Shin, daidai ne mu biya Kaisar haraji, ko kuwa?
Suka aiko almajiransu wurinsa tare da waɗansu mutanen Hirudus, suka ce, “Malam, ai, mun sani kai mai gaskiya ne, sai koyar da tafarkin Allah sosai kake yi, ba ka kuma zaɓen kowa, don ka ɗauki kowa da kowa daidai.
Duk mazaunan duniya kuma, za su yi mata sujada, wato, duk wanda, tun farkon duniya, ba a rubuta sunansa a Littafin Rai na Ɗan Ragon nan da yake Yankakke ba.
Amma waɗannan mutane, kamar daddobi marasa hankali suke, masu bin abin da jikinsu ya ba su kawai, waɗanda aka haifa, don a kama a kashe, har suna kushen abubuwan da ba su fahinta ba, lalle kuwa za su hallaka a sanadin ɓacin nan nasu,
Haka Ubangiji ya ce, “Ku tsaya kan hanyoyi, ku duba, Ku nemi hanyoyin dā, inda hanya mai kyau take, Ku bi ta, don ku hutar da rayukanku. Amma suka ce, ‘Ai, ba za mu bi ta ba.’
Za a yi babbar karauka a can, Za a kira ta, “Hanyar Tsarki.” Ba mai zunubi da zai taɓa bi ta wannan hanya, Ba wawayen da za su ruɗar da waɗanda suke tafiya can.
Gama waɗansu mutane sun saɗaɗo a cikinku, waɗanda tun zamanin dā aka ƙaddara ga hukuncin nan, marasa bin Allah ne, masu mai da alherin Allah dalilin aikata fajirci, suna kuma ƙin makaɗaicin Ubangijinmu Yesu Almasihu.
Haka kuma Saduma da Gwamrata, da birane kewayensu, waɗanda su ma suka dulmuya cikin fasikanci da muguwar sha'awa ta jiki, an nuna su domin ishara, suna shan hukuncin madawwamiyar wuta.