2 Bitrus 1:21 - Littafi Mai Tsarki21 Domin ba wani annabcin da ya taɓa samuwa ta nufin mutum, sai dai mutane ne Ruhu Mai Tsarki yake izawa, Allah yana magana ta bakinsu. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202021 Gama annabci bai taɓa samo tushensa daga nufin mutum ba, sai dai mutane sun yi magana daga Allah yayinda Ruhu Mai Tsarki ya bishe su. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Bisa ga ka'idar da tsohonsa Dawuda ya tsara, sai Sulemanu ya karkasa firistoci ƙungiya ƙungiya domin su yi hidima, Lawiyawa kuma bisa ga matsayinsu na yin yabo da hidima a gaban firistoci, kamar yadda aka wajabta kowace rana. Matsaran ƙofa kuma aka karkasa su ƙungiya ƙungiya bisa ga yawan ƙofofin, gama haka Dawuda, mutumin Allah, ya umarta.