5 Wane ne yake nasara da duniya, in ba wanda ya gaskata Yesu Ɗan Allah ba ne?
5 Wa ya cin nasara a kan duniya? Sai wanda ya gaskata cewa Yesu Ɗan Allah ne.
Kowa ya bayyana yarda, cewa Yesu Ɗan Allah ne, sai Allah yă dawwama a cikinsa, shi kuma a cikin Allah.
Kowa da yake gaskata Yesu shi ne Almasihu, haifaffen Allah ne. Kowa yake ƙaunar mahaifi kuwa, yana ƙaunar ɗa kuma.
Sai Yesu ya ce masa, “In zan iya? Ai, dukkan abu mai yiwuwa ne ga mai ba da gaskiya.”
Mun kuma sani Ɗan Allah ya zo, ya yi mana baiwar fahimta domin mu san shi wanda yake na gaskiya. Mu kuwa muna a cikinsa, shi da yake na gaskiya, wato Ɗansa Yesu Almasihu. Shi ne Allah na gasikya da kuma rai madawwami.
Filibus ya ce, “In dai ka ba da gaskiya da zuciya ɗaya, ai, sai a yi maka.” Bābān ya amsa ya ce, “Na gaskata Yesu Almasihu ɗan Allah ne.”