Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Yohanna 5:16 - Littafi Mai Tsarki

16 Kowa ya ga ɗan'uwansa yana yin zunubin da bai kai ga mutuwa ba, sai ya yi masa addu'a. Saboda mai addu'ar nan kuwa, Allah zai ba da rai ga waɗanda suka yi zunubin da bai kai ga mutuwa ba. Akwai zunubin da yake na mutuwa. Ban ce a yi addu'a domin wannan ba.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

16 Kowa ya ga ɗan’uwansa yana yin zunubin da bai kai ga mutuwa ba, sai yă yi masa addu’a. Ta dalilin mai addu’an nan kuwa, Allah zai ba da rai ga mai yin zunubin da bai kai ga mutuwa ba. Akwai zunubin da yakan kai ga mutuwa. Ban ce a yi addu’a domin wannan ba.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Yohanna 5:16
32 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Don haka kada ka yi wa waɗannan mutane addu'a. Kada ka yi kuka ko addu'a dominsu, gama ba zan kasa kunne gare su ba, ko da sun yi kirana a lokacin wahalarsu.”


Idan mutum ya yi wa wani laifi, Allah yakan kāre shi, amma idan mutum ya yi wa Ubangiji zunubi, wa zai kāre shi?” Amma ba su ji maganar mahaifinsu ba, gama Ubangiji ya riga ya yi shirin kashe su.


Kowa ya kushe wa Ɗan Mutum, ā gafarta masa, amma wanda ya saɓi Ruhu Mai Tsarki, ba za a gafarta masa ba.


Sai Ubangiji ya ce mini, “Kada ka yi addu'a domin lafiyar jama'an nan.


“Kai kuwa, Irmiya kada ka yi wa mutanen nan addu'a. Kada ka yi kuka ko addu'a dominsu, kada ka roƙe ni, gama ba zan ji ka ba.


Amma mutumin da ya yi laifi da gangan, ko shi ɗan ƙasa ne, ko kuma baƙo ne, ya sāɓi Ubangiji, sai a kashe shi,


Ya ce, “Idan na sami tagomashi a gare ka, ya Ubangiji, ina roƙonka, ka yi tafiya tare da mu, ko da yake jama'a masu taurinkai ne, ka gafarta laifinmu, da zunubinmu, ka sa mu zama abin gādonka.”


Ibrahim ya yi addu'a ga Allah, Allah kuwa ya warkar da Abimelek, da matarsa, da bayinsa mata, har kuma suka sami haihuwa.


Yanzu fa, sai ka mayar wa mutumin da matarsa, gama shi annabi ne, zai yi maka addu'a, za ka kuwa rayu. In kuwa ba ka mayar da ita ba, ka sani hakika za ka mutu, kai, da dukan abin da yake naka.”


Saboda wannan Allah ya ce zai hallaka jama'arsa, Amma Musa, zaɓaɓɓen bawansa, ya yi godo ga Allah, Allah kuwa ya huce, bai hallaka su ba.


Ni, roƙo nake yi dominsu. Ba duniya nake roƙa wa ba, sai dai su waɗanda ka ba ni, domin su naka ne.


Sai na nemi mutum a cikinsu wanda zai gina garun ya tsaya a hauren garun a gabana, domin kada in hallaka ƙasar, amma ban sami kowa ba.


Sai Musa ya roƙi Ubangiji, ya ce, “Ina roƙonka, ya Allah, ka warkar da ita.”


Iskandari maƙerin farfarun nan ya yi mini mugunta ƙwarai, Ubangiji zai yi masa sakayyar aikinsa.


Suka ce wa Sama'ila, “Ka yi wa bayinka roƙo ga Ubangiji Allahnka don kada mu mutu, gama mun ƙara wa kanmu zunubi da muka roƙa a yi mana sarki.”


Duk rashin adalci zunubi ne. Akwai kuma zunubin da ba na mutuwa ba.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ