Mun sani, mun kuma gaskata ƙaunar da Allah yake yi mana. Allah shi ne ƙauna wanda yake a dawwame cikin kauna kuwa, ya dawwama a cikin Allah ke nan, Allah kuma a cikinsa.
Daga ƙarshe kuma, 'yan'uwa, sai wata rana. Ku kammala halinku. Ku kula da roƙona, ku yi zaman lafiya da juna, ku yi zaman salama, Allah mai zartar da ƙauna da salama kuwa zai kasance a tare da ku.
Ta haka sai a ga waɗanda suke 'ya'yan Allah, da kuma waɗanda suke 'ya'yan Iblis, wato duk wanda ba ya aikata adalci, ba na Allah ba ne, haka kuma wanda ba ya ƙaunar ɗan'uwansa.