11 Wannan shi ne jawabin da kuka ji tun farko, cewa dai mu ƙaunaci juna,
11 Wannan shi ne saƙon da kuka ji tun farko. Ya kamata mu ƙaunaci juna.
“Wannan fa shi ne umarnina, cewa ku ƙaunaci juna kamar yadda na ƙaunace ku.
Yanzu kuma ina roƙonki, uwargida, ba cewa wani sabon umarni nake rubuto miki ba, sai dai wanda muke da shi tun farko ne, cewa mu ƙaunaci juna.
Ya ku ƙaunatattuna, sai mu ƙaunaci juna, domin ƙauna ta Allah ce. Duk mai ƙauna kuwa haifaffen Allah ne, ya kuma san Allah.
Wannan kuma shi ne umarnin da muka samu daga gare shi, cewa mai ƙaunar Allah, sai ya ƙaunaci ɗan'uwansa kuma.
Fiye da kome kuma, ku himmantu ga ƙaunar juna, domin ƙauna takan yafe laifofi masu ɗumbun yawa.
Daga ƙarshe kuma dukanku ku haɗa hankulanku, ku zama masu juyayi, masu ƙaunar 'yan'uwa, masu tausayi, da kuma masu tawali'u.
Ku yi zaman ƙauna kamar yadda Almasihu ya ƙaunace mu, ya kuma ba da kansa dominmu, sadaka mai ƙanshi, hadaya kuma ga Allah.
Wannan shi ne jawabin da muka ji a gunsa, muke sanar da ku cewa Allah haske ne, ba kuwa duhu gare shi ko kaɗan.
A game da ƙaunar 'yan'uwa kuma, ba lalle sai wani ya rubuto muku ba. Ai, ku kanku ma, Allah ya koya muku ku ƙaunaci juna.
Da yake kun tsarkake ranku kuna yi wa gaskiya biyayya har kuna nuna sahihiyar ƙauna ga 'yan'uwa, sai ku himmantu ga ƙaunar juna da zuciya ɗaya.
Alhali kuwa manufar gargaɗinmu ƙauna ce, wadda take bulbulowa daga tsarkakakkiyar zuciya, da lamiri mai kyau, da kuma sahihiyar bangaskiya.
Ku ɗauki wahalar juna, ta haka za ku cika shari'ar Almasihu.
sai ya tashi daga cin abincin, ya ajiye mayafinsa, ya ɗauko ɗan zane ya yi ɗamara da shi.
Ya ku ƙaunatattuna, tun da yake Allah ya ƙaunace mu haka, ai, mu ma ya kamata mu ƙaunaci juna.