Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Yohanna 2:8 - Littafi Mai Tsarki

8 Har wa yau sabon umarni nake rubuto muku, wanda yake tabbatacce ga Almasihu, da kuma gare ku, domin duhu yana shuɗewa, hakikanin haske kuma yana haskakawa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

8 Duk da haka ina rubuta muku sabon umarni; ana ganin gaskiyar umarnin a cikinsa da kuma cikinku, gama duhu yana shuɗewa, haske na gaskiya kuwa yana haskakawa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Yohanna 2:8
31 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

domin dā ku duhu ne, amma a yanzu ku haske ne a cikin Ubangiji. Ku yi zaman mutanen haske,


Dare fa ya ƙure, gari ya kusa wayewa. Sai mu watsar da ayyukan duhu, mu yi ɗamara da kayan ɗamara na haske.


Sabon umarni nake ba ku, shi ne ku ƙaunaci juna. Kamar yadda na ƙaunace ku, haka ku ma, ku ƙaunaci juna.


Sai Yesu ya ƙara musu da cewa, “Ni ne Hasken duniya. Wanda yake bi na ba zai yi tafiya a duhu ba, amma zai sami hasken rai,”


Akwai hakikanin haske mai shigowa duniya da yake haskaka kowane mutum.


Na zo duniya a kan ni haske ne, domin duk mai gaskatawa da ni kada ya yi zaman duhu.


Wannan kuma shi ne umarnin da muka samu daga gare shi, cewa mai ƙaunar Allah, sai ya ƙaunaci ɗan'uwansa kuma.


Amma ku da kuke yi mini biyayya, ikon cetona zai fito muku kamar rana. Zai kawo warkarwa kamar hasken rana. Za ku fita kuna tsalle kamar 'yan maruƙan da aka fisshe su daga garke.


Ya ku ƙaunatattuna, tun da yake Allah ya ƙaunace mu haka, ai, mu ma ya kamata mu ƙaunaci juna.


wadda a yanzu aka bayyana ta bayyanar Mai Cetonmu Almasihu Yesu, wanda ya shafe mutuwa, ya kuma bayyana rai da rashin mutuwa, ta wurin bishara.


Domin kun san alherin Ubangijinmu Yesu Almasihu, ko da yake shi mawadaci ne, sai ya zama matalauci sabili da ku, domin ta wurin talaucinsa ku wadata.


domin ka buɗe musu ido, su juyo daga duhu zuwa haske, daga kuma mulkin Shaiɗan zuwa wurin Allah, domin su sami gafarar zunubai, da kuma gādo tare da dukan tsarkaka saboda sun gaskata da ni.’ ”


Dā kam, Allah ya kawar da kai ga zamanin jahilci, amma yanzu yana umartar dukkan mutane a ko'ina su tuba,


Domin yă haskaka na zaune cikin duhu, Da waɗanda suke zaune a bakin mutuwa, Domin ya bishe mu a hanyar salama.”


Kai ne mafarin dukan rai, Saboda haskenka ne kuma, muke ganin haske.


Ubangiji ne haskena da cetona, Ba zan ji tsoron kowa ba. Ubangiji yana kiyaye ni daga dukan hatsari, Ba zan ji tsoro ba.


Yesu ya ce musu, “Haske na tare da ku har ɗan lokaci kaɗan na gaba. Ku yi tafiya tun haske na tare da ku, kada duhu ya ci muku. Mai tafiya a cikin duhu bai san inda yake tafiya ba.


Mazaunan duhu sun ga babban haske, Mazaunan bakin mutuwa da fargabarta, Haske ya keto musu.”


Jama'ar da suka yi tafiya cikin duhu, Sun ga babban haske! Suka zauna a inuwar mutuwa, Amma yanzu haske ya haskaka su.


Ubangiji shi ne makiyayinmu, sarkinmu mai daraja, Yakan sa mana albarka, da alheri, da daraja, Ba ya hana kowane abu mai kyau ga waɗanda suke aikata abin da yake daidai.


To gare shi ne kuka gaskata da Allah, wanda ya ta da shi daga matattu, ya kuma ɗaukaka shi, domin bangaskiyarku da begenku su kasance ga Allah.


Umarninsa kuwa shi ne mu gaskata da sunan Ɗansa Yesu Almasihu, mu kuma ƙaunaci juna, kamar yadda ya umarce mu.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ