Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Yohanna 2:5 - Littafi Mai Tsarki

5 Amma duk wanda yake kiyaye maganarsa, wannan kam, hakika yana ƙaunar Allah, cikakkiyar ƙauna. Ta haka muka tabbata muna cikinsa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

5 Amma in wani ya yi biyayya da maganarsa, ƙaunar Allah ta zama cikakkiya ke nan a cikinsa. Ta haka muka san cewa muna cikinsa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Yohanna 2:5
32 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Yesu ya amsa masa ya ce, “Kowa yake ƙaunata, zai kiyaye maganata, Ubana kuwa zai ƙaunace shi, za mu zo wurinsa mu zauna tare da shi.


Duk wanda ya san umarnaina, yake kuma binsu, shi ne mai ƙaunata. Mai ƙaunata kuwa, Ubana zai ƙaunace shi, ni kuma zan ƙaunace shi, in bayyana kaina gare shi.”


Amma ya ce, “I, amma albarka tā fi tabbata ga waɗanda suke jin Maganar Allah, suke kuma kiyaye ta.”


Duk mai bin umarnin Allah kuwa a dawwame yake cikinsa, Allah kuma a cikinsa. Ta haka muka tabbata ya dawwama a cikinmu, saboda Ruhun da ya ba mu.


Masu farin ciki ne waɗanda suke bin umarnansa, Waɗanda suke yi masa biyayya da zuciya ɗaya.


Wannan yana nuna jimirin tsarkaka, masu kiyaye umarnin Allah da kuma bangaskiya ga Yesu.


Ta haka muku sani muna ƙaunar 'ya'yan Allah, wato, in muna ƙaunar Allah, muna kuma bin umarninsa.


Ni ne itacen inabin, ku kuwa rassan. Wanda ya zauna a cikina, ni kuma a cikinsa, shi ne mai yin 'ya'ya da yawa. Domin in ba game da ni ba, ba za ku iya kome ba.


Zan sa ruhuna a cikinku, in sa ku bi dokokina, ku kiyaye ka'idodina.


Ba tsoro ga ƙauna, amma cikakkiyar ƙauna takan yaye tsoro. Tsoro kansa ma azaba ne, mai jin tsoro kuwa ba shi da cikakkiyar ƙauna,


Ina kira gare ka, Ka cece ni, zan bi ka'idodinka!


Saboda haka, duk wanda yake na Almasihu sabuwar halitta ne, tsohon al'amari duk ya shuɗe, ga shi, kome ya zama sabo.


Macijin kuwa ya yi fushi da matar, ya tafi ya ɗaura yaƙi da sauran zuriyarta, wato, waɗanda suke kiyaye umarnin Allah, suke kuma shaidar Yesu.


Mun kuma sani Ɗan Allah ya zo, ya yi mana baiwar fahimta domin mu san shi wanda yake na gaskiya. Mu kuwa muna a cikinsa, shi da yake na gaskiya, wato Ɗansa Yesu Almasihu. Shi ne Allah na gasikya da kuma rai madawwami.


Gama Allah ne ya sa kuka zama na Almasihu Yesu, Allah ne kuma ya sa Almasihu ya zama hikima a gare mu. Ta wurin Almasihu ne kuma muka sami adalci, da tsarkakewa da fansa.


Saboda haka a yanzu, ba sauran kayarwa ga waɗanda suke na Almasihu Yesu.


Ka gani, ashe, bangaskiyarsa da aikatawarsa duka yi aiki tare, har ta wurin aikatawar nan bangaskiyarsa ta kammala.


Shi da bai san zunubi ba, Allah ya mai da shi zunubi saboda mu, domin mu mu sami adalcin Allah ta wurinsa.


Duk wanda suke cin naman jikina, yake shan jinina, a cikina yake zaune, ni kuma a cikinsa.


Muddin ka kiyaye umarnin sarki gidanka lafiya, mai hikima yakan yi abu, ya kuma san lokacin yi da hanyar da ta dace da yinsa.


Masu farin ciki ne waɗanda suke biyayya da umarnansa, Waɗanda kullayaumi suke aikata abin da yake daidai!


“Yanzu ku matasa, ku kasa kunne gare ni, Ku yi abin da na ce, za ku yi farin ciki.


Kai ka ba mu dokokinka, Ka kuwa faɗa mana mu kiyaye su da aminci.


Saurayi wanda ya kiyaye doka mai basira ne shi, amma wanda yake abuta da 'yan iska zai zama mai jawo wa mahaifinsa kunya.


Don jama'arsa su yi biyayya da dokokinsa, Su kuma kiyaye umarninsa. Ku yabi Ubangiji!


Ta haka ne ƙauna ta cika a gare mu, har mu kasance da amincewa a ranar shari'a, domin kamar yadda yake, haka mu ma muke a duniyar nan.


Ƙauna kuwa ita ce mu bi umarninsa. Umarnin kuwa, shi ne kamar yadda kuka ji tun farko, cewa ku yi zaman ƙauna.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ