Domin shi Allah wanda ya ce, “Haske yă ɓullo daga duhu ya haskaka,” shi ne ya haskaka zukatanmu domin a haskaka mutane su san ɗaukakarsa a fuskar Yesu Almasihu.
Bayan shan wahalarsa, zai sāke yin murna, Zai fahimta wahalar da ya sha ba ta banza ba ce, Shi ne bawana, adali, Zai ɗauki hukuncin mutane masu yawa, Ya sa su zama mutanena amintattu.
Ya ku dattawa, ina rubuto muku ne domin kun san shi, shi wanda yake tun fil'azal. Ya ku samari, ina rubuto muku ne domin kun ci nasara a kan Mugun nan. Ya ku 'yan yara, ina rubuto muku ne domin kun san Uba.