Gama masu ruɗi da yawa sun fito duniya, waɗanda ba sa bayyana yarda, cewa Yesu Almasihu ya bayyana da jiki, irin wannan shi ne mai ruɗi, magabcin Almasihu.
Ku lura fa, kada kowa ya ribace ku ta hanyar iliminsa na yaudarar wofi, bisa ga al'adar mutane kawai, wato, bisa ga al'adun duniyar nan, ba bisa ga koyarwar Almasihu ba.
Kada ku yarda kowane mutum ya ɓata ku, da cewa shi wani abu ne saboda, ya ga wahayi, ya kuma lazamta da yin tawali'un ƙarya, in ji shi kuma yana yi wa mala'iku sujada. Irin wannan mutum kumbura kansa yake yi ba dalili, sai ta son zuciya irin na halin mutuntaka,
“Domin sun ɓad da mutanena suna cewa, ‘Salama,’ sa'ad da ba salama, sa'ad da kuma mutanen suke gina garu marar aminci, sai annabawan nan su shafe shi da farar ƙasa,