Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Yohanna 2:12 - Littafi Mai Tsarki

12 Ya ku 'ya'yana ƙanana, ina rubuto muku ne domin an gafarta muku zunubanku saboda sunansa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

12 Ina rubuta muku, ’ya’yana ƙaunatattu, domin an gafarta muku zunubanku saboda sunansa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Yohanna 2:12
22 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Shi ne duk annabawa suka yi wa shaida, cewa albarkacin sunansa duk mai gaskatawa da shi zai sami gafarar zunubai.”


Saboda haka, 'yan'uwa, sai ku sani albarkacin mutumin nan ne ake sanar da ku gafarar zunubanku.


Ta gare shi ne muka sami fansa albarkacin jininsa, wato yafewar laifofinmu, bisa ga yalwar alherin Allah,


Ba kuma samun ceto ga wani, domin ba wani suna duk duniyan nan da aka bayar cikin mutane, wanda lalle ta wurinsa ne za mu sami ceto.”


Amma duk da haka ya cece su, kamar yadda ya alkawarta, Domin ya nuna ikonsa mai girma.


wanda ta gare shi ne muka sami fansa, wato, gafarar zunubanmu.


Ka cika alkawarinka, ya Ubangiji, ka gafarta zunubaina, gama suna da yawa.


In kuwa muna zaune a haske, kamar yadda shi yake cikin haske, muna tarayya da juna ke nan, jinin Yesu Ɗansa kuma yana tsarkake mu daga dukkan zunubi.


Muna kuma rubuto muku wannan ne domin farin cikinmu ya zama cikakke.


a kuma yi wa dukan al'ummai wa'azi su tuba, a gafarta musu zunubansu saboda sunansa. Za a kuwa fara daga Urushalima.


Da Yesu ya ga bangaskiyarsu sai ya ce, “Malam, an gafarta maka zunubanka.”


Ina rubuto muku, ba don ba ku san gaskiya ba ne, a'a, sai domin kun san ta, kun kuma sani gaskiya ba ta haifar ƙarya.


Irmiya ya ce, “Ko da yake zunubanmu su ne shaidunmu, Ya Ubangiji, ka yi taimako saboda sunanka! Gama kāsawarmu ta yi yawa, Domin mun yi maka zunubi.


Ya ku ƙaunatattuna, ba fa wani sabon umarni nake rubuto muku ba, a'a, daɗaɗɗen umarnin nan ne wanda kuke da shi tun farko. Daɗaɗɗen umarnin nan kuwa, ai, shi ne maganar da kuka ji.


Ya ku 'ya'yana ƙanana, ina rubuto muku wannan ne domin kada ku yi zunubi. In kuwa wani ya yi zunubi, muna da Mai Taimako a gun Uba, wato, Yesu Almasihu mai adalci.


In kuwa muka bayyana zunubanmu, to, shi mai alkawari ne, mai adalci kuma, zai kuwa gafarta mana zunubanmu, ya tsarkake mu daga dukkan rashin adalci.


Ku yi wa juna kirki, kuna tausayi, kuna yafe wa juna kamar yadda Allah ya yafe muku ta wurin Almasihu.


Waɗansunku ma dā haka suke, amma an wanke ku, an tsarkake ku, an kuma kuɓutar da ku, da sunan Ubangiji Yesu Almasihu, da kuma Ruhun Allahnmu.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ