Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Yohanna 1:6 - Littafi Mai Tsarki

6 In mun ce muna tarayya da shi, alhali kuwa muna zaune a duhu, mun yi ƙarya ke nan, ba ma aikata gaskiya.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

6 In muka ce muna zumunci da shi amma muna tafiya cikin duhu, ƙarya muke yi, kuma ba ma rayuwa bisa ga gaskiya.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Yohanna 1:6
25 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Kowa ya ce yana ƙaunar Allah, alhali kuwa yana ƙin dan'uwansa, to, maƙaryaci ne. Don wanda ba ya ƙaunar ɗan'uwansa da yake gani, ba dama ya ƙaunaci Allah wanda bai taɓa gani ba.


Kowa ya ce ya san shi, ba ya kuwa bin umarninsa, maƙaryaci ne, gaskiya kuma ba ta tare da shi.


In mun ce ba mu yi zunubi ba, mun ƙaryata shi ke nan. Maganarsa kuma ba ta tare da mu.


mutane waɗanda suka bar zaman adalci don su zauna cikin duhun zunubi,


Sai Yesu ya ƙara musu da cewa, “Ni ne Hasken duniya. Wanda yake bi na ba zai yi tafiya a duhu ba, amma zai sami hasken rai,”


Yesu ya ce musu, “Haske na tare da ku har ɗan lokaci kaɗan na gaba. Ku yi tafiya tun haske na tare da ku, kada duhu ya ci muku. Mai tafiya a cikin duhu bai san inda yake tafiya ba.


Ya ku 'yan'uwana, ina amfani mutum ya ce yana da bangaskiya, alhali kuwa ba ya aikin da zai nuna ta? Anya, bangaskiyar nan tāsa ta iya cetonsa?


Na zo duniya a kan ni haske ne, domin duk mai gaskatawa da ni kada ya yi zaman duhu.


to, shi wannan da muka ji, muka kuma gani, shi ne dai muke sanar da ku, domin ku ma ku yi tarayya da mu. Hakika kuwa tarayyar nan tamu da Uba ne, da kuma Ɗansa Yesu Almasihu.


Amma kowa yake tafiya da dare yakan yi tuntuɓe, don ba haske a gare shi!”


To, amma wani zai ce, “Ai, kai kana da bangaskiya, ni kuwa sai aikatawa.” To, nuna mini bangaskiya, taka ba tare da aikatawa ba, ni kuma in nuna maka aikatawata, tabbatar bangaskiyata.


“Waɗanne irin jahilai ne ku, wawaye! Kuna zaune cikin duhu, Ga shi, ba adalci a duniya sam!


In mun ce ba mu da zunubi, ruɗin kanmu muke yi, gaskiya kuwa ba ta tare da mu.


waninku kuma ya ce musu, “To, ku sauka lafiya, Allah ya ba ci, da sha, da tufatarwa” ba tare da kun biya musu bukata ba, ina amfanin haka?


A ranar nan da yawa za su ce mini, ‘Ya Ubangiji, ya Ubangiji, ashe, ba mu yi annabci da sunanka ba? Ba mu fitar da aljannu da sunanka ba? Ba mu kuma yi ayyukan al'ajabi masu yawa da sunanka ba?’


ta wurin makircin waɗansu maƙaryata, waɗanda aka yi wa lamirinsu lalas.


Ba ruwanka da alƙalai azzalumai, marasa gaskiya, Waɗanda suka mai da rashin gaskiya ita ce gaskiyarsu,


Ku ba ku san shi ba, amma ni na san shi. Da na ce ban san shi ba, da na zama maƙaryaci kamarku. Amma na san shi, ina kuma kiyaye magana tasa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ