1 Yohanna 1:3 - Littafi Mai Tsarki3 to, shi wannan da muka ji, muka kuma gani, shi ne dai muke sanar da ku, domin ku ma ku yi tarayya da mu. Hakika kuwa tarayyar nan tamu da Uba ne, da kuma Ɗansa Yesu Almasihu. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20203 Muna yin muku shelar abin da muka gani, muka kuma ji ne, domin ku ma ku yi zumunci tare da mu. Zumuncinmu kuwa yana tare da Uba da kuma Ɗansa, Yesu Kiristi. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
su kuwa sani ni ne wanda yake hukunta musu. “Amma zan bar waɗansu, in aika da su ga al'ummai da manisantan ƙasashe inda ba a ji labarin sunan da na yi ba, ba a kuwa ga girmana da ikona ba, wato zuwa Tarshish, da Libiya, da Lidiya, duk da gwanayen maharbanta, Rosh da Tubal, da kuma Helas. Za su ba da labarin girmana ga waɗannan al'ummai.