Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Timoti 6:3 - Littafi Mai Tsarki

3 Duk wanda yake wata koyarwa dabam, bai kuwa yarda da sahihiyar maganar Ubangijinmu Yesu Almasihu, da kuma koyarwar da ta dace da bautar Allah ba,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

3 In wani yana koyarwar ƙarya bai kuma yarda da sahihiyar koyarwar Ubangijinmu Yesu Kiristi da kuma koyarwa ta tsoron Allah ba,

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Timoti 6:3
19 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Kamar yadda na roƙe ka, ka dakata a Afisa sa'ad da za ni ƙasar Makidoniya, ka gargaɗi waɗansu mutane kada su koyar da wata koyarwa dabam,


da fasikai, da masu luɗu, da masu sace mutane, da maƙaryata, da masu shaidar zur, da kuma duk sauran abin da ya sāɓa sahihiyar koyarwar nan,


mai riƙe da tabbatacciyar maganar nan kankan, daidai yadda aka koya masa, domin yă iya ƙarfafa wa waɗansu zuciya da sahihiyar koyarwa, ya kuma ƙaryata waɗanda suka yi musunta.


Don lokaci zai zo da mutane ba za su jure sahihiyar koyarwa ba, amma saboda kunnensu yana ƙaiƙayi, sai su taro masu koyarwa da za su biya musu muradinsu.


Ina roƙonku, 'yan'uwa, ku yi hankali fa da masu raba tsakani, saɓanin koyarwar da kuka koya, suna sa tuntuɓe. Ku yi nesa da su.


Daga Bulus, bawan Allah, kuma manzon Yesu Almasihu, saboda bangaskiyar zaɓaɓɓun Allah, da kuma inganta sanin gaskiyar ibadarmu,


Ka yi koyi da sahihiyar maganar da ka ji daga gare ni, da bangaskiya da ƙauna da take ga Almasihu Yesu.


Waɗansu sun kauce wa waɗannan al'amura, har sun bauɗe, sun shiga zancen banza.


Saboda haka, kowa ya ƙi yarda da wannan, ba mutum ya ƙi ba, amma Allah ya ƙi, shi da yake ba ku Ruhunsa Mai Tsarki.


kuna koya musu su kiyaye duk iyakar abin da na umarce ku. Ga shi, ni kuma kullum ina tare da ku har zuwa matuƙar zamani.”


Kalmomin alheri suna kawo rai, amma maganganun ƙiyayya suna karya zuciyar mutum.


Maganar nan tabbatacciya ce. Ina so ka ƙarfafa waɗannan abubuwa ƙwarai, don waɗanda suka ba da gaskiya ga Allah su himmantu ga aiki nagari, waɗannan abubuwa kuwa masu kyau ne, masu amfani kuma ga mutane.


Suka ce, “Na Kaisar ne.” Sa'an nan ya ce musu, “To, sai ku ba Kaisar abin da yake na Kaisar, ku kuma ba Allah abin da yake na Allah.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ