Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Timoti 5:8 - Littafi Mai Tsarki

8 Duk wanda bai kula da danginsa ba, tun ba ma iyalinsa ba, ya mūsa wa bangaskiya ke nan, ya kuma fi marar ba da gaskiya mugunta.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

8 In wani bai kula da danginsa ba, musamman iyalinsa na kurkusa, ya mūsunta bangaskiya ke nan, ya kuma fi marar ba da gaskiya muni.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Timoti 5:8
19 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

To, saboda haka, in hali ya yi, sai mu kyautata wa kowa, tun ba ma waɗanda suke jama'ar masu ba da gaskiya ba.


Ga shi, na yi shirin zuwa wurinku, zuwa na uku, ba kuwa zan nauyaya muku ba, don ba abinku nake nema ba, ku nake nema, domin ba yara ne da ɗaukar nauyin iyayensu ba, sai dai iyaye ne da ɗaukar nauyin yaran.


Ku ci abincinku tare da mayunwata, ku kuma shigo da matalauta, marasa mahalli a cikin gidajenku. Idan kuma kun ga wanda yake tsirara, ku sa masa sutura, kada kuma ku ɓoye fuskokinku ga 'yan'uwanku.


Suna cewa sun san Allah, amma suna sāɓa masa ta wurin aikinsu. Abin ƙyama ne su, kangararru, ko kaɗan ba su da wani amfani a wajen yin aiki nagari.


To, ku da kuke mugaye ma, kuka san yadda za ku ba 'ya'yanku kyautar kyawawan abubuwa, balle Ubanku na Sama da zai ba da abubuwan alheri ga masu roƙonsa?


suna riƙe da siffofin ibada, amma suna sāɓa wa ikonta. Ka yi nesa da irin waɗannan mutane.


Gama kafin in zo, kana da 'yan kima ne, ga shi, sun ƙaru da yawa, Ubangiji kuwa ya sa maka albarka duk inda na juya. Amma yanzu, sai yaushe zan hidimta wa nawa gidan?”


“ ‘Na san ayyukanka. Ka ga, na bar maka ƙofa a buɗe, wadda ba mai iya rufewa. Na dai san ƙarfinka kaɗan ne, duk da haka, kā kiyaye maganata, ba ka yi musun sanin sunana ba.


“ ‘Na san a inda kake da zama, wato, a inda kursiyin Shaiɗan yake. Duk da haka kuwa, ka tsaya a gare ni, ba ka bar yi mini bangaskiya ba, ko a zamanin Antibas amintaccen mashaidina, wanda aka kashe a cikinku, a inda Shaiɗan yake zaune.


Amma fa annabawan ƙarya sun bayyana a cikin jama'a, kamar yadda za a sami malaman ƙarya a cikinku, waɗanda za su saɗaɗo da maɓarnacciyar fanɗarewa, har ma su ƙi Mamallakin da ya fanso su, suna jawo wa kansu hallaka farat ɗaya.


Da ba domin na zo na yi musu magana ba, da ba su da zunubi. Amma yanzu kam, ba su da wani hanzari a kan zunubinsu.


Gama waɗansu mutane sun saɗaɗo a cikinku, waɗanda tun zamanin dā aka ƙaddara ga hukuncin nan, marasa bin Allah ne, masu mai da alherin Allah dalilin aikata fajirci, suna kuma ƙin makaɗaicin Ubangijinmu Yesu Almasihu.


Ina kuma jiyayyar Almasihu da iblis? Me kuma ya haɗa mai ba da gaskiya da marar ba da gaskiya?


In kuma ya ƙi sauraronsu, sai ka shaida wa ikilisiya. In kuma har ya ƙi sauraron ikilisiyar, ka maishe shi kamar bare, ko mai karɓar haraji.”


Amma ɗan'uwa yakan kai ƙarar ɗan'uwa, gaban marasa ba da gaskiya kuma?


In mun jure, za mu yi mulki ma tare da shi, In mun yi musun saninsa, shi ma zai yi musun saninmu,


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ