Yadda ta ɗaukaka kanta, ta yi almubazzaranci, Haka ku ma ku saka mata da azaba, da baƙin ciki gwargwadon haka. Tun da yake a birnin zuciyarta ta ce, ‘Ni sarauniya ce, a zaune nake, Ni ba gwauruwa ba ce, Ba ni da baƙin ciki kuma har abada!’
“Ka kuma rubuta wa mala'ikan ikkilisiyar da take a Sardisu haka, ‘Ga maganar mai Ruhohin Allah guda bakwai, da kuma taurarin nan bakwai. “ ‘Na san ayyukanka, kai rayayye ne, alhali kuwa matacce ne kai.
Ubangiji ya ce, “Babila, ki sauko daga kan gadon sarautarki, Ki zauna a ƙasa cikin ƙura. Dā ke budurwa ce, birnin da ba a yi nasara da shi ba! Amma ba sauran taushi da kuma rashin ƙarfi! Ke baiwa ce yanzu!
A maimakon haka sai kuka yi dariya, kuka yi biki. Kuka yanka tumaki da shanu don ku ci, kuka sha ruwan inabi. Kuka ce, “Gara mu ci mu sha! Gobe za mu mutu.”
Sa'an nan Sama'ila ya ce, “Ku kawo mini Agag Sarkin Amalekawa.” Sai Agag ya taho wurinsa, yana rawar jiki don tsoro, yana cewa a ransa, “Hakika, azabar mutuwa ta fi ɗaci.”
Matar kirki mai taushin zuciya wadda take tare da ku wadda ba za ta sa tafin ƙafarta a ƙasa ba saboda taushin zuciyarta da kyakkyawan halinta, za ta ƙi ƙaunataccen mijinta, da ɗanta, da 'yarta.
A cikinsu kuwa akwai masu saɗaɗawa su shiga gidajen mutane, suna rinjayar mata marasa wayo, waɗanda zunubi ya sha kansu, muguwar sha'awa iri iri kuma ta ɗauke musu hankali,