Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Timoti 5:4 - Littafi Mai Tsarki

4 In wata gwauruwa tana da 'ya'ya ko jikoki, sai su koya, ya wajaba su fara nuna wa danginsu bautar Allah da suke yi, su kuma sāka wa iyayensu da alheri. Wannan abin karɓa ne a gun Allah.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

4 Amma in gwauruwa tana da ’ya’ya ko jikoki, to, sai su fara koyon yin ayyukan addininsu ga danginsu, ta haka za su sāka wa iyayensu da kakanninsu, gama wannan yakan gamshi Allah.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Timoti 5:4
18 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Yusufu ya bai wa mahaifinsa da 'yan'uwansa da dukan iyalin gidan mahaifinsa abinci, bisa ga yawan 'ya'yansu.


Wannan kyakkyawan abu ne, kuma abin karɓa ne a gun Allah Mai Cetonmu,


Sai ya koma Nazarat tare da su, yana yi musu biyayya. Uwa tasa kuwa na riƙe da dukan abubuwan nan a ranta.


'Ya'yanta sukan tashi su gode mata, mijinta kuma yana yabonta.


Ta ɗauka, ta koma gari, ta nuna wa surukarta abin da ta kalato. Ta kuma kawo mata sauran abincin da ta ci ta ƙoshi har ta rage.


Sai Rut, mutuniyar Mowab, ta ce wa Na'omi, “Bari in tafi, in yi kalan hatsi a gonar wanda ya yarda in yi.” Na'omi ta ce mata, “Ki tafi, 'yata.”


Ubangiji Mai Runduna ya ce, “Zan fāɗa wa Babila da yaƙi, in lalata ta, ba abin da zan bari, ko yara, ba wanda zai ragu. Ni, Ubangiji, na faɗi wannan.


Ba shi da zuriya, da sauran waɗanda suka ragu da rai.


Yana da 'ya'ya maza arba'in, da jikoki maza talatin, suna hawan jakai saba'in. Abdon ya shugabanci Isra'ilawa shekara takwas.


Yakubu kuma ya zauna a ƙasar Masar shekara goma sha bakwai, don haka kwanakin Yakubu, wato shekarun ransa, shekara ce ɗari da arba'in da bakwai.


Duk mace mai bi, da take da dangi gwauraye mata, sai ta taimake su, kada a nauwaita wa ikkilisiya, don ikkilisiyar ta samu ta taimaki gwauraye marasa mataimaka.


Lalle ne a kwaɓe su, tun da yake suna jirkitar da jama'a gida gida, ta wurin koyar da abin da bai kamata ba, don neman ƙazamar riɓa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ