Sun dai fita daga cikinmu, amma dā ma can ba namu ba ne. Don in da namu ne, da har yanzu suna tare da mu. Amma sun fita ne domin a bayyana dukansu ba namu a ciki.
Sai aka jefa ƙaton macijin nan a ƙasa, wato macijin nan na tun dā dā, wanda ake kira Ibilis da Shaiɗan, mayaudarin dukkan duniya, aka jefa shi a duniya, mala'ikunsa ma aka jefa su tare da shi.
yana magana a kan wannan, kamar yadda yake yi a dukan wasiƙunsa, akwai waɗansu abubuwa a cikin masu wuyar fahinta, waɗanda jahilai da marasa kintsuwa suke juya ma'anarsu, kamar yadda suke juya sauren Littattafai, ta haka suke jawo wa kansu hallaka.