In kuwa wani yana jin yunwa, sai yă ci a gida, kada yă zamana taronku ya jawo muku hukunci. Batun sauran abubuwa kuwa, zan ba da umarni a kai sa'ad da na zo.
Amma kada ka lasafta gwauraye masu ƙuruciya waɗanda mazansu suka mutu, a cikin gwaurayen, don in zuciyarsu ta kasa daurewa a game da wa'adin da suka yi da Almasihu, sai su so yin aure,
Banda haka kuma sukan koyi zaman banza, suna zirga-zirga gida gida. Ba ma kawai masu zaman banza za su zama ba, har ma sai su zama matsegunta, masu shishigi, suna faɗar abin da bai kamata ba.