9 Maganar nan tabbatacciya ce, ta kuma cancanci a karɓe ta ɗungum.
9 Wannan magana tabbatacciya ce wadda ta cancanci cikakkiyar karɓa.
Maganar nan tabbatacciya ce, ta kuma cancanci a karɓe ta ɗungum cewa, “Almasihu Yesu ya shigo duniya ne domin ceton masu zunubi,” ni ne kuwa babbansu.
Sai ubangijinsa ya ce masa, ‘Madalla, bawan kirki, mai aminci. Kā yi gaskiya a kan ƙaramin abu, zan ɗora ka a kan mai yawa. Ka zo ku yi farin ciki tare da ubangidanka.’