Don miji marar ba da gaskiya, a tsarkake yake a wajen matarsa. Mace marar ba da gaskiya kuma, a tsarkake take a wajen mijinta. In ba haka ba, zai zamana 'ya'yanku ba masu tsarki ba ne, amma ga hakika masu tsarki ne.
Ga masu tsarkin rai duk al'amarinsu mai tsarki ne, marasa tsarkin rai kuwa marasa ba da gaskiya, ba wani al'amarinsu da yake mai tsarki, da zuciyarsu da lamirinsu duka marasa tsarki ne.
Allah kuwa ya yi dabbobin gida bisa ga irinsu, da kuma na jeji, manya da ƙanana, da kowane irin mai rarrafe bisa ƙasa bisa ga irinsa. Allah kuwa ya ga yana da kyau.