Waɗanda suke da iyayengiji masu ba da gaskiya, kada su raina su, domin su 'yan'uwa ne a gare su. Sai ma su ƙara bauta musu, tun da yake waɗanda suke moron aikin nan nasu masu ba da gaskiya ne, ƙaunatattu kuma a gare su. Ka koyar da waɗannan abubuwa, ka kuma yi gargaɗinsu.
Maganar nan tabbatacciya ce. Ina so ka ƙarfafa waɗannan abubuwa ƙwarai, don waɗanda suka ba da gaskiya ga Allah su himmantu ga aiki nagari, waɗannan abubuwa kuwa masu kyau ne, masu amfani kuma ga mutane.
ka yi wa'azin Maganar Allah, ka dimanta a kai ko da yaushe, kana shawo kan mutane, kana tsawatarwa, kana ƙarfafa zukata, a game da matuƙar haƙuri da kuma koyarwa.