11 Mace ta riƙa koyo da kawaici da matuƙar biyayya.
11 Ya kamata mace ta riƙa koyo cikin natsuwa da cikakkiyar biyayya.
Amma fa ina so ku fahimci cewa, shugaban kowane mutum Almasihu ne, shugaban kowace mace kuwa mijinta ne, shugaban Almasihu kuma Allah ne.
Haka kuma, ku matan aure, ku yi biyayya ga mazanku, don ko waɗansunsu ba su bi maganar Allah ba, halin matansu yă shawo kansu, ba tare da wata magana ba,
su kuma kasance natsattsu, masu tsarkin rai, masu kula da gida, masu alheri, masu biyayya ga mazansu, don kada a kushe Maganar Allah.
Ku matan aure, ku bi mazanku yadda ya dace a cikin Ubangiji.
Ga matar kuwa ya ce, “Zan tsananta naƙudarki ainun, da azaba za ki haifi 'ya'ya, duk da haka muradinki zai koma ga mijinki, zai kuwa mallake ki.”
Sa'ad da aka ji dokar sarki, wadda zai yi a dukan babbar ƙasarsa, dukan mata za su girmama mazansu, ƙanana da manya.”
sai dai su yi aiki nagari, yadda ya dace da mata masu bayyana shaidar ibadarsu.