Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Tessalonikawa 5:8 - Littafi Mai Tsarki

8 Amma da yake mu na rana ne, sai mu natsu, muna saye da sulken bangaskiya da ƙauna, muna begen samun ceto, shi ne kuma kwalkwakinmu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

8 Amma da yake mu na rana ne, bari mu zama masu kamunkai, sanye da bangaskiya da ƙauna kamar sulke, begen cetonmu kuma kamar hular kwano.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Tessalonikawa 5:8
25 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Don haka, sai ku yi ɗamara, ku natsu, ku sa zuciyarku sosai a kan alherin da zai zo muku a bayyanan Yesu Almasihu.


Ku yi ɗamara da dukan makamai na Allah, don ku iya dagewa gāba da kissoshin Iblis.


Ya rufe ƙirjinsa da sulken adalci, da kwalkwalin ceto a kansa. Ya sa rigar ɗaukar fansa, ya yafa alkyabbar ikonsa.


Begen nan kuwa da muke da shi, kamar anka yake ga rai, kafaffe, tabbatacce, shi ne kuma yake shiga har can ciki bayan labulen,


To, a yanzu abubuwan nan uku sun tabbata, bangaskiya, da bege, da kuma ƙauna, amma duk mafi girma a cikinsu ita ce ƙauna.


Domin duk mutanen haske kuke, na rana kuma. Mu ba na dare ko na duhu ba ne.


In kuwa muna zaune a haske, kamar yadda shi yake cikin haske, muna tarayya da juna ke nan, jinin Yesu Ɗansa kuma yana tsarkake mu daga dukkan zunubi.


Amma ku kabila ce zaɓaɓɓiya, ƙungiyar firistocin babban Sarki, tsattsarkar al'umma, jama'ar mallakar Allah, domin ku sanar da mafifitan al'amuran wannan da ya kirawo ku daga cikin duhu, kuka shiga maɗaukakin haskensa.


da maganar gaskiya, da kuma ikon Allah. Muna riƙe da makaman adalci dama da hagu.


Yana da kyau a jira ceton Ubangiji da natsuwa,


Salamar Allah Uba da ta Ubangiji Yesu Almasihu su tabbata ga 'yan'uwa, tare da ƙauna game da bangaskiya.


Gama mu, ta wurin ikon Ruhu, muke ɗokin cikar begen nan namu na samun adalcin Allah saboda bangaskiya.


Me ya sa nake baƙin ciki? Me ya sa nake damuwa? Zan dogara ga Allah, Zan ƙara yabonsa, Mai Cetona, Allahna.


Me ya sa ni ɓacin rai haka? Me ya sa ni damuwa? Zan dogara ga Allah. Har yanzu ma zan yabe shi, Mai Cetona, Allahna.


Me ya sa nake baƙin ciki haka? Me ya sa nake damuwa ƙwarai? Zan dogara ga Allah, Zan sāke yin yabonsa, Mai Cetona, Allahna.


To, Ubangijinmu Yesu Almasihu kansa, da kuma Allah Ubanmu, wanda ya ƙaunace mu, ya kuma ba mu madawwamiyar ta'aziyya da kyakkyawan bege ta wurin alherinsa,


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ