Sa'ad da aka karanta wasiƙar nan a gabanku, ku sa a karanta ta kuma a gaban ikilisiyar da take a Lawudikiya, ku kuma ku karanta tasu, wato ta Lawudikiyawa.
Sai waɗansu Yahudawa masu yawo gari gari, matsubbata, suka yi ƙoƙarin kama sunan Ubangiji Yesu ga masu baƙaƙen aljannu, suna cewa, “Mun umarce ku da sunan Yesun nan da Bulus yake wa'azi.”
Saboda haka, ya ku 'yan'uwa tsarkaka, ku da kuke da rabo a kiran nan basamaniya, sai ku tsai da zuciya ga Yesu, Manzo, da kuma Babban Firist na bangaskiyar da muke shaidawa,
Masu dukiyar duniyar nan kuwa ka gargaɗe su kada su nuna alfarma, kada kuwa su dogara da dukiya marar tabbata, sai dai ga Allah, wanda yake ba mu kome a yalwace don mu ji daɗinsa.