Daga ƙarshe kuma, 'yan'uwa, ko mene ne yake na gaskiya, ko mene ne abin girmamawa, ko mene ne daidai, ko mene ne tsattsarka, ko mene ne abin ƙauna, ko mene ne daɗɗaɗar magana, in ma da wani abu mafifici, ko abin da ya cancanci yabo, a kan waɗannan abubuwa za ku yi tunani.
kuna ceton waɗansu kuna fizgo su daga wuta. Waɗansu kuma ku ji tausayinsu, amma tare da tsoro kuna ƙyamar ko da tufafin da halinsu na mutuntaka ya ƙazantar.
Kuna iya tsira idan kuna faɗar gaskiya kuna kuma yin abin da yake daidai. Kada ku gwada ikonku don ku cuci talakawa, kada kuwa ku karɓi rashawa. Kada ku haɗa kai da masu shiri su yi kisankai, ko su aikata waɗansu mugayen abubuwa.
Allah kansa, mai zartar da salama, yă tsarkake ku sarai, ya kuma kiyaye ruhunku da ranku da jikinku ƙalau, ku kasance marasa abin zargi a ranar komowar Ubangijinmu Yesu Almasihu.
Sa'ad da ya kwanta, sai ki lura da inda ya kwanta, sa'an nan ki tafi, ki buɗe mayafinsa a wajen ƙafafunsa, ki kwanta a ciki. Zai kuwa faɗa miki abin da za ki yi.”
Sai ta kwanta a wajen ƙafafunsa har safiya. Sa'an nan ta tashi tun da jijjifi kafin a iya gane fuskar mutum, gama ba ya so a sani mace ta zo masussukar.