Kada ku biye wa zamanin nan, amma ku bar halinku ya sāke, ta wurin sabunta hankalinku ɗungum, don ku tabbatar da abin da Allah yake so, wato nufinsa kyakkyawa, abin karɓa, cikakke kuma.
To, waɗannan Yahudawa kam, sun fi na Tasalonika dattaku, domin sun karɓi Maganar hannu biyu biyu, suna ta nazarin Littattafai kowace rana, su ga ko abin haka yake.
Daga ƙarshe kuma, 'yan'uwa, ko mene ne yake na gaskiya, ko mene ne abin girmamawa, ko mene ne daidai, ko mene ne tsattsarka, ko mene ne abin ƙauna, ko mene ne daɗɗaɗar magana, in ma da wani abu mafifici, ko abin da ya cancanci yabo, a kan waɗannan abubuwa za ku yi tunani.
Don haka, sai ka tuna da abin da ka karɓa ka kuma ji, ka kiyaye shi, sa'an nan ka tuba. In ba za ka yi tsaro ba, zan zo kamar ɓarawo, ba kuwa za ka san a lokacin da zan auko maka ba.
Don haka, ya 'yan'uwana, ƙaunatattu, ku tsaya a kafe, kullum kuna himmantuwa ga aikin Ubangiji, domin kuwa kun san famar da kuke yi saboda Ubangiji ba a banza take ba.
Ku zauna a cikina, ni kuma a cikinku. Kamar yadda reshen inabi, ba ya iya 'ya'ya shi kaɗai, sai ko ya zauna itacen inabin, haka ku ma ba za ku iya ba, sai kun zauna a cikina.
Ga amsar da za ku ba su, ku ce, “Ku kasa kunne ga koyarwar Ubangiji. Kada ku kasa kunne ga 'yan bori. Gama abin da suka faɗa muku ba zai amfane ku ba.”
“ ‘Na san ayyukanka, da famarka, da jimirinka, da yadda ba ka iya haƙurce wa mugaye, ka kuma gwada waɗanda suke ce da kansu manzanni, alhali kuwa ba su ba ne, ka tarar na ƙarya ne.
A cikinsu kuwa akwai masu saɗaɗawa su shiga gidajen mutane, suna rinjayar mata marasa wayo, waɗanda zunubi ya sha kansu, muguwar sha'awa iri iri kuma ta ɗauke musu hankali,