Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Tessalonikawa 5:18 - Littafi Mai Tsarki

18 Ku godiya ga Allah a kowane hali, domin shi ne nufin Allah a game da ku ta wurin Almasihu Yesu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

18 ku yi godiya cikin kowane hali, gama wannan shi ne nufin Allah dominku cikin Kiristi Yesu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Tessalonikawa 5:18
11 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Kullum ku riƙa gode wa Allah Uba da sunan Ubangijinmu Yesu Almasihu a kan ko mene ne.


Kada ku damu da kome, sai dai a kowane hali ku sanar da Allah bukatunku, ta wurin yin addu'a da roƙo, tare da gode wa Allah.


Kome kuke yi, a game da magana ko aikatawa, ku yi duka da sunan Ubangiji Yesu, kuna gode wa Allah Uba ta wurinsa.


To, a koyaushe, sai mu yi ta yabon Allah ta wurinsa, sadakar da muke miƙawa ke nan, wato mu yabe shi, muna ta ɗaukaka sunansa.


domin a nan gaba yă ƙarasa sauran zamansa na jiki ba tare da biye wa muguwar sha'awar zuciya ba, sai dai nufin Allah.


ya ce, “Ban shigo duniya da kome ba, ba kuma zan fita cikinta da kome ba. Ubangiji ya bayar, shi ne kuma ya karɓe, yabo ya tabbata ga sunansa.”


Zan yi godiya ga Ubangiji kullayaumin, Faufau ba zan taɓa fasa yabonsa ba.


Domin nufin Allah ne ku toshe jahilcin marasa azanci ta yin aiki nagari.


Duniyar kuwa tana shuɗewa da mugayen burinta, amma mai aikata nufin Allah zai dawwama har abada.


Gama wannan shi ne nufin Allah, wato ku yi zaman tsarki, ku guje wa fasikanci,


Sa'ad da Daniyel ya sani an sa hannu a dokar, sai ya tafi gidansa. Ya buɗe tagogin benensa waɗanda suke fuskantar Urushalima. Sau uku kowace rana yakan durƙusa ya yi addu'a, yana gode wa Allahnsa kamar yadda ya saba.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ