Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




1 Tessalonikawa 4:9 - Littafi Mai Tsarki

9 A game da ƙaunar 'yan'uwa kuma, ba lalle sai wani ya rubuto muku ba. Ai, ku kanku ma, Allah ya koya muku ku ƙaunaci juna.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

9 Yanzu kuwa game da ƙaunar ’yan’uwa, ba ma bukata mu rubuta muku, gama ku kanku Allah ya riga ya koya muku ku ƙaunaci juna.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




1 Tessalonikawa 4:9
30 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Wannan shi ne jawabin da kuka ji tun farko, cewa dai mu ƙaunaci juna,


A game da ƙaunar 'yan'uwa kuwa, ku ƙaunaci juna gaya. A wajen ba da girma, kowa yă riga ba ɗan'uwansa.


Umarninsa kuwa shi ne mu gaskata da sunan Ɗansa Yesu Almasihu, mu kuma ƙaunaci juna, kamar yadda ya umarce mu.


Wannan kuma shi ne umarnin da muka samu daga gare shi, cewa mai ƙaunar Allah, sai ya ƙaunaci ɗan'uwansa kuma.


Amma ga zancen ainihin lokaci ko rana, ba lalle sai an rubuto muku kome ba.


To, duk taron da suka ba da gaskiya kuwa nufinsu ɗaya ne, ra'ayinsu ɗaya, ba kuma waninsu da ya ce abin da ya mallaka nasa ne, sai dai kome nasu ne baki ɗaya.


Mai ƙaunar ɗan'uwansa, a haske yake zaune, ba kuma wani sanadin sa tuntuɓe a gare shi.


bin Allah da son 'yan'uwa, son 'yan'uwa kuma da ƙauna.


Fiye da kome kuma, ku himmantu ga ƙaunar juna, domin ƙauna takan yafe laifofi masu ɗumbun yawa.


Daga ƙarshe kuma dukanku ku haɗa hankulanku, ku zama masu juyayi, masu ƙaunar 'yan'uwa, masu tausayi, da kuma masu tawali'u.


“Wannan shi ne alkawarin da zan yi da su, Bayan kwanakin nan, in ji Ubangiji, Zan sa shari'una a birnin zuciyarsu, In kuma rubuta su a allon zuciyarsu,”


Amma Mai Taimako, Ruhu Mai Tsarki, wanda Uba zai aiko da sunana, shi ne zai koya muku kome, ya kuma tuna muku duk abin da na faɗa muku.


Abu mai kyau ne, mai daɗi kuma, Ga jama'ar Allah su zauna tare kamar 'yan'uwa!


Na biyu kuma kamarsa yake, ‘Ka ƙaunaci ɗan'uwanka kamar kanka.’


Mutum ba zai ƙara koya wa maƙwabcinsa, ko ɗan'uwansa cewa, ‘Ka san Ubangiji’ ba, gama su duka za su san ni, tun daga ƙarami har zuwa babba. Zan gafarta musu laifofinsu, ba kuwa zan ƙara tunawa da zunubansu ba.”


Kuna mantawa da Ubangiji wanda ya halicce ku, Wanda ya shimfiɗa sammai, Ya kuma kafa harsashin ginin duniya? Don me za ku yi ta jin tsoron fushin waɗanda suke zaluntarku, Da waɗanda suke shiri su hallaka ku? Fushinsu ba zai taɓa yi muku kome ba!


Wanda ya ci ta a rana ta uku ɗin, zai zama da laifi, domin ya tozartar da abu mai tsarki na Ubangiji, sai a raba wannan mutum da jama'a.


Amma wannan shi ne alkawarin da zan yi da mutanen Isra'ila bayan waɗancan kwanaki, ni Ubangiji na faɗa. Zan sa dokokina a cikinsu, zan rubuta su a zukatansu, zan zama Allahnsu, su kuma za su zama jama'ata.


Ba sai lalle na rubuto muku zancen gudunmawa ga tsarkaka ba,


Saboda haka ɗaukacin waɗanda suka kammala a cikinmu, sai su bi wannan ra'ayi. In kuwa a game da wani abu ra'ayinku ya sha bambam, to, Allah zai bayyana muku wannan kuma.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ